Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na NNPP a Kano, Ta Bai Wa Dan APC Kujerarsa
- Kotun sauraron kararrakin zaben majalisa a jihar Kano ta soke nasarar jam'iyyar NNPP a zaben dan majalisa mai wakiltan Tarauni
- Kotu ta tsige Mukhtar Yarima daga kan kujerarsa saboda zargin kirkirar takardar kammala karatunsa na Firamare
- Ta kuma ayyana Hafizu Kawu na APC a matsayin wanda ya lashe zabe sannan ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta gaggauta ba shi takardar shaidar cin zabe
Jihar Kano - Kotun zaben majalisar dokoki na kasa da jiha wacce ke zama a Kano ta soke zaben mamba mai wakiltan mazabar Tarauni a majalisar dokokin tarayya, Mukhtar Yarima.
Kotu ta fatattaki Yarima wanda ya kasance dan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) kan zargin kirkirar takardar karatu na bogi.
Daily Nigerian ta rahoto cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Mista Yarima a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu inda ya lallasa Hafizu Kawu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sakamakon rashin amincewa da sakamakon zaben, Mista Kawu ya shigar da kara kotu, inda yake kalubalantar nasarar dan takarar na NNPP kan hujjar cewa ya kirkiri takardar shaidar kammala karatunsa na Firamare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Makarantar Hausawa ta nesanta kanta da satifiket din Yarima
Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, kwamitin mutun uku na kotun zaben, ya zartar da cewar an kirkiri takardar shaidar kammala karatun firamare da Mista Yarima ya gabatarwa INEC ne.
Kotun zaben ta riki cewa makarantar firamare na Hausawa, wanda Yarima ya yi ikirarin cewa ya halarta ta nesanta kanda da takardar shaidar kammala karatun domin dai babu sunan wanda ake kara a cikin rijistarta.
Kotu ta mayar da dan takarar APC a kan kujerar
Kotun ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta ayyana dan takarar na APC, Hafizu Kawu a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ta gabatar masa da takardar shaidar cin zabe ba tare da bata lokaci ba, rahoton Leadership.
Kotu Ta Tsare Fitaccen Malamin Addini Kan Zargin Mallakar Bindiga AK-47 A Coci, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
Ku tuna cewa, Garba Galadanci, baturen zaben mazabar Tarauni a babban zaben 2023, ya ayyana Yarima na NNPP a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Tarauni bayan ya samu kuri'u 26,273, inda Kawu na APC ya samu kuri'u 15,931.
Da gaske Tinubu ya dakatar da kotunan zabe?
A wani labarin kuma, mun ji cewa a ranar 26 ga watan Yuli, wata kafar yada labarai, Igbo Times Magazine, ta wallafa wani labari da ke ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umurnin dakatar da dukkan kotunan da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, Abuja.
An rahoto cewa ya dakatar da kotunan ne saboda fargabar kada a sauke shi.
Asali: Legit.ng