An Caccaki Godswill Akpabio Kan Batun Kuɗaɗen Shakatawar Sanatoci Da Ya Sanar a Zaman Majalisa

An Caccaki Godswill Akpabio Kan Batun Kuɗaɗen Shakatawar Sanatoci Da Ya Sanar a Zaman Majalisa

  • A ranar Litinin, 7 ga watan Agusta ne Majalisar Dattawan Najeriya ta yi zama domin tabbatar da ministocin Tinubu
  • Sai dai da aka zo gab da ƙarshen zaman ne shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio ya yi ɓarin zance
  • Ya yi batun wasu kuɗaɗe da aka warewa sanatocin ba tare da sanin cewa ana kallonsa a talabijin ba

Abuja - A ranar Litinin ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya jagoranci zaman da aka tabbatar da ministocin Tinubu 45 daga cikin 48 da ya turo.

Sai dai a yayin da zaman ya kusa zuwa ƙarshe, Godswill Akpabio ya yi wata magana da aka haska a bidiyo da ta janyo cece-kuce.

Wani bidiyo da Legit.ng ta gano a shafin Twitter na wani mai suna @JaypeeGeneral, ya nuna inda Akpabio ya yi maganar ba tare da lura da cewa ana kallonsa a talabijin ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Bukaci Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio Ya Gaggauta Yin Murabus

Bidiyon Akpabio ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta
Bidiyon Akpabio ya janyo masa suka a kafafen sada zumunta. Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Maganar Akpabio da ta janyo muhawara

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a Intanet, an ga shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio yana gabatar da jawabi bayan kamamala zaman majalisa na ranar Litinin wanda suka tabbatar da ministoci a cikinsa.

Akpabio ya sanar da tafiya hutun majalisar ta dattawa zuwa ranar 26 ga watan Satumba mai kamawa.

Biyo bayan sanarwar ba da hutun da Akpabio ya yi ne kuma ya bayyana cewa, akwai wasu 'yan kuɗaɗe da aka ware don bai wa kowane sanata damar shaƙatawa yayin hutun.

Akpabio ya yi ƙoƙarin sauya batun biyo bayan fahimta da ya yi cewa ana kallonsa kai tsaye a gidajen talabijin.

Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi martani kan bidiyon na Akpabio

Masu amfani da kafar sada zumunta ta Twitter, sun yi zazzafan martani dangane da kalaman na Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

Sunayen Ministocin Tinubu 2 Da Aka Tabbatar Duk Da Suna Da Wata Babbar Matsala a Tattare Da Su

@Uchenna_Azorji ya ce:

“A yayin da magoya bayan Tinubu ke yawace birnin Legas a ƙasa.”

@JohnCro3 ya ce:

“Ka duba fa, gaskiya akwai ciwo mutum ya taso a najeriya.”

@kingship1980 ya ce:

“Ya Ubangiji, me muka yi ne da muke fuskantar waɗannan ƙalubale, ka yafe mana.”

@roebonline ya ce:

“Yan siyasar Najeriya da cin hanci kamar 5&6 ne. Ya sauya batun bayan ganowa da ya yi ana kallonsa a talabijin. Allah ya albarkacin Najeriya.”

MURIC ta nemi Majalisar Dattawa ta bayyana dalilin ƙin tabbatar da El-Rufai

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan buƙatar da kungiyar kare hakkin Musulmi ta ƙasa (MURIC), ta aikawa Majalisar Dattawan Najeriya kan dalilin kin tabbatar da El-Rufai.

MURIC ta miƙa wannan buƙata ne biyo bayan ƙin tabbatar da tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai da Majalisar ta ƙi yi a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng