ECOWAS Za Ta Sake Zama Don Yanke Hukunci Kan Nijar Ranar Alhamis

ECOWAS Za Ta Sake Zama Don Yanke Hukunci Kan Nijar Ranar Alhamis

  • A ranar Lahadin da ta gabata ne wa'adin da ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar ya cika
  • Ta nemi sojojin su miƙa mulki ga hamɓararren shugaban ƙasa Muhammed Bazoum cikin kwanaki bakwai
  • Shugaban ECOWAS Bola Tinubu, ya sanya ranar Alhamis a matsayin ranar da za su sake zama don tattauna mataki na gaba

Abuja - A ranar Lahadi ne wa'adin da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta bai wa sojojin Nijar na su mayar da mulki hannu hamɓararren shugaban kasar Muhammed Bazoum.

A yau Litinin, shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar ta ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da cewa kungiyar za ta yi zama a ranar Alhamis don tattaunawa kan mataki na gaba kamar yadda aka wallafa a shafin ECOWAS na Twitter.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugabannin ECOWAS Sun Gana Bayan Janar Tchiani Ya Yi Biris Da Wa'adin Da Suka Ba Shi

ECOWAS za ta sake zama don tattauna batutuwan Nijar
ECOWAS za ta sake zama ranar Alhamis don tattaunawa batutuwan juyin mulkin Nijar. Hoto: ECOWAS - Cedeao
Asali: Twitter

ECOWAS za ta tattauna kan abubuwan da ke waka a Nijar

ECOWAS ta ce za ta tattauna ne kan batutuwan da suka shafi siyasa da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a jamhuriyar Nijar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin da ƙungiyar ta diɓarwa sojojin na Nijar na su mayar da mulki hannun farar hula ke cika.

Mutanen Najeriya da na Nijar, musamman ma waɗanda ke zaune a jihohin da suke kan iyakokin ƙasar na fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin ƙasashen biyu a dalilin wannan dambarwa da ake ciki.

Sojojin Nijar sun sanar da rufe sararin samaniyar ƙasar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan rufe sararin samaniyar Nijar da sojojin da suka yi juyin mulki suka yi.

An bayyana cewa sojojin na Nijar sun ɗauki wannan mataki ne domin kare sararin samanaiyarsu daga duk wata barazana ta hare-hare na mamaya da akan iya kawo musu.

Kara karanta wannan

Fargabar Yaƙi: Jerin Jihohin Najeriya 7 da Suka Haɗa Boda da Jamhuriyar Nijar

Bello Yabo ya ce za su nemi majalisa ta tsige Tinubu idan ya tura sojoji Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan iƙirarin da fitaccen malamin nan na addinin Muslunci Bello Yabo ya yi, na cewa za su sa majalisa ta tsige Tinubu idan ya dage kan sai ya tura sojoji Nijar.

Yabo ya ce abinda ya kamata Najeriya ta yi shi ne ba da shawara ba amfani da ƙarfin soji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng