Kotun Amurka Ta Yi Fatali Da Karar Atiku Abubakar Ta Neman Takardun Karatun Tinubu
- Wata kotun ƙasar Amurka ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar akan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Ƙarar da Atiku ya shigar, yana neman ganin takardun karatun Tinubu a jami'ar jihar Chicago, kotun 'Circuit Court of Cook County' ta yankin Illinois ta yi fatali da ita
- Mai shari'a Patrick J. Heneghan na kotun ya yi fatali da ƙarar ba tare da nuna wani bambanci ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
A yayin da ake jiran hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, kotun 'Circuit Court of Cook County', ta yankin Illinois a Amurka, ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya shigar.
Ƙarar da Atiku ya shigar a lokacin zaɓen 2023 yana neman takardun karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jami'ar Chicago, an yi fatali da ita, jaridar Leadership ta rahoto.
Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Kulle Sararin Samaniyar Kasar Yayin Da ECOWAS Ke Barazanar Amfani Da Karfin Soja
A cikin ƴan kwanakin nan Atiku ya shigar da ƙara yana neman a aike da sammaci ga jami'ar, amma kafin zuwan ranar sauraron ƙarar, ya janye ƙarar da ya shigar a gaban kotun.
Atiku vs Tinubu: Hukuncin kotun Amurka
A cewar takardun kotun 'Circuit Court' na ranar 31 ga watan Yuli wadanda jaridar The Punch ta samo a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta, mai shari'a Patrick J. Heneghan ya yi fatali da ƙarar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin hukuncin, alƙalin ya bayyana cewa tun da mai shigar da ƙara ya janye sammaci da ya nema, saboda haka jami'ar jihar Chicago (CSU) ba za a aike mata da sammacin da aka nema ba a cikin ƙarar.
Dalilin da ya sanya kotun Amurka ta yi fatali da ƙarar Atiku kan Tinubu
A cikin ƙarar, tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar shi ne mai shigar da ƙara, sannan jami'ar jihar Chicago (CSU) ita ake ƙara.
Da yanke hukunci kan ƙarar wacce Atiku Abubakar ya shigar akan jami'ar jihar Chicago, mai shari'a Heneghan ya bayyana cewa an yi fatali da ƙarar ba tare da nuna wani bambanci ba, sannan ya warware dukkanin wani lamari da ya shafi ƙarar a gaban kotun, cewar rahoton Thisday.
Tinubu Ya Samu Ƴabo Daga Jigon APC
A wani labarin kuma, wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Zamfara ya yaba wa shugaban ƙasa Ahmed Tinubu bisa zaɓo Matawalle domin zama minista.
Anas Abdullahi Kaura ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya fi sauran shugabannin da suka taɓa mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng