Rikicin PDP: Atiku, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Shiga Ganawa a Abuja

Rikicin PDP: Atiku, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Shiga Ganawa a Abuja

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa sun halarci taron masu ruwa da tsakin PDP a Abuja ranar Asabar
  • Gwamnonin jam'iyyar PDP da dama sun je wurin taron kuma ana tsammanin sauran suna kan hanya zasu ƙariso
  • Wannan gana wa dai zata fi maida hankali ne kan abubuwan da ke wakana a cikin PDP da hanyar da za a bi don farfaɗo da jam'iyyar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, Alhaji Atiku Abubakar, na ganawar sirri da gwamnonin PDP yanzu haka a Abuja.

Abokin takarar Atiku a zaben da ya gabata kuma tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, na cikin mahalarta taron wanda ke gudana a Anguwar Asokoro.

Taron masu ruwa da tsakin PDP.
Rikicin PDP: Atiku, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Shiga Ganawa a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa na tsawon zango biyu, ya tabbatar da haka a wani rubutu mai haɗe da Hotuna da ya wallafa a shafinsa na facebook.

Kara karanta wannan

Kariɓ Bayani: Jami'an DSS Sun Titsiye Sakataren Gwamnatin Jihar APC Kan Abu 2, Bayanai Sun Fito

Wannan taro na masu ruwa da tsakin PDP ba zai rasa nasaba da yanayin yadda harkokin babbar jam'iyyar adawa ke tafiya a yanzu ba, rigingimun cikin gida sun baibaye ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana tsammanin taron zai tattauna kan yadda za a sake fasalin jam'iyyar PDP ta yadda zata farfaɗo bayan kashin da ta sha a babban zaɓen 2023 da ya gabata.

Duk da ana tsammanin dukkan gwamnonin jam'iyyar PDP zasu halarci taron na masu ruwa da tsaki, zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton gwamnoni 7 ne suka isa wurin.

Gwamnonin da aka gani sun halarci wurin taron

Gwamnonin da aka hanga sun kama wuri a ɗakin taron sun haɗa da Bala Muhammed na jihar Bauchi, Sheriff Oborevwori na jihar Delta, da Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.

Sauran sun ƙunshi Dauda Lawal na jihar Zamfara, Godwin Obaseki na jihar Edo, Ademola Adeleke na jihar Osun da kuma Douye Diri na jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Kus-Kus Da Mataimakin Tinubu a Villa Kan Muhimmin Batun da Ya Shafi Arewa

Sai dai ba bu tabbacin ko Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ɗaya daga cikin gwamnonin G-5 da suka yaƙi Atiku a babban zaɓen 2023, zai halarci taron na yau Asabar.

Sauran mahalarta taron sun ƙunshi shugaban PDP na rikon kwarya, Umar Damagum, Sakataren jam'iyya, Samuel Anyanwu, Sakataren watsa labarai, Debo Ologunagba da sauran mambobin NWC.

Jami'an DSS Sun Titsiye Sakataren Gwamnatin Jihar APC Kan Babban Abu

A wani rahoton na daban kuma Hukumar DSS ta fara bincikar sakataren gwamnatin jihar Ogun, Tokunbo Talabi, na hannun daman gwamna Dapo Abiodun.

Jami'ai sun titsiye Talabi ne bisa zargin hannu a buga takardun zabe lokacin zaɓen 2023 da kuma badaƙalar kuɗin COVID19.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262