“Allah Ya Nuna Mani”: Shin Shugaban Kasa Tinubu Zai Kammala Wa’adinsa a Mulki? Malamin Addini Ya Yi Hasashe

“Allah Ya Nuna Mani”: Shin Shugaban Kasa Tinubu Zai Kammala Wa’adinsa a Mulki? Malamin Addini Ya Yi Hasashe

  • Prophet Chibuzo Nkemakolam ya yi hasashe mai kyau a kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Prophet Nkemakolam, wanda ke zaune a yankin kudu maso gabashin Najeriya, ya ce kotu ko yan majalisar tarayya ba za su tsige shugaban kasar ba
  • Malamin addinin ya kuma yi hasashen abun da zai faru a gwamnatin Bola Tinubu, inda ya bukaci yan Najeriya da su amshi kaddararsu

Isieke, jihar Ebonyi - Prophet Chibuzo Nkemakolam, shugaban cocin Throne of Power Ministry, ya ce Allah ya nuna masa watanni biyu da suka wuce cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai yi shugabanci har 2031.

Fasto Nkemakolam ya bayyana cewa ba za a tsige shugaban kasa Tinubu ba kuma haka ba zai mutu ba a kan karagar mulki.

Malamin addini ya ce Tinubu zai kammala mulkinsa lafiya
“Allah Ya Nuna Mani”: Shin Shugaban Kasa Tinubu Zai Kammala Wa’adinsa a Mulki? Malamin Addini Ya Yi Hasashe Hoto: Chibuzo Nkemakolam, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

'Yan Najeriya za su rayu na tsawon shekaru 16 a hannun wadanda ba a so': Fasto Nkemakolam

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Cikakken Bayani Kan Shiyyoyin Da Aka Zabo Mutanen Da Aka Bayyana Sunayensu

Malamin addinin ya kuma yi hasashen cewa Tinubu zai mika shugabancin Najeriya ga wani shugaba dan arewa, wanda zai yi mulki na wasu shekaru takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu shine shugaban kasar Najeriya na 16. Ya yi gwamnan jihar Lagas daga 1999 zuwa 2007, sannan sanatan Lagas ta yamma a jahuriya ta uku.

Fasto Nkemakolam ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 2 ga Agusta:

“Na san kiristoci da yawa suna fatan ina ma ace shugaban kasar ya bar ofishinsa da wuri imma ya mutu ko a tsige shi. Amma Allah ya nuna min inda ya yi mulki cikakke na tsawon shekaru takwas ba a nan kawai ba, ya mika wa wani dan Arewa mulki wanda ya kara shekaru takwas. Ta tashi shekaru goma sha shida na mulki a hannun da ba a so. Kuma na ga wani dan Kudu da ya kulla yarjejeniya da shugaban kasa mai ci don ya karbi mulki daga hannun sa bayan wa'adin mulkinsa cikin takaici."

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

Inyamurai sun nemi gwamnan jihar Neja ya basu mukami a gwamnatinsa

A wani labari na daban, mun ji cewa al'ummar Igbo mazauna jihar Neja sun yi kira ga Gwamna Mohammed Bago da ya nada daya daga cikinsu a majalisarsa saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen tattara kudaden shiga a jihar.

Sun kuma bayyana goyon bayansu ga gwamnan sannan sun ce hakan zai yi daidai da alkawarin da ya dauka na tafiya da kowa a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng