Igbo Sun Nemi Gwamnan Neja Ya Basu Manyan Mukaman Gwamnati

Igbo Sun Nemi Gwamnan Neja Ya Basu Manyan Mukaman Gwamnati

  • An bukaci gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago da ya baiwa dan kabilar Igbo mukami a majalisarsa
  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo reshen jihar ta arewa maso gabas ta ce Inyamurai sun fi kowa bayar da gudunmawa wajen kawo ci gaba ta bangaren tattara kudaden shiga a jihar
  • Sun ce majalisar Bago ba za ta cika ba idan har babu dan kabilar Igbo a cikinta domin sun fi kowace kabila kawo kudaden shiga

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Niger - Al'ummar Igbo mazauna jihar Neja sun yi kira ga Gwamna Mohammed Bago da ya nada daya daga cikinsu a majalisarsa saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen tattara kudaden shiga a jihar.

Sun kuma bayyana goyon bayansu ga gwamnan sannan sun ce hakan zai yi daidai da alkawarin da ya dauka na tafiya da kowa a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

An bukaci gwamnan jihar Neja ya ba yan kabilar Igbo mukami
Samun Wuri: Igbo Sun Nemi Gwamnan Arewa Ya Nada Su A Babban Mukamin Gwamnati Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Majalisar Bago ba za ta cika ba idan babu dan Igbo, Kungiyar Ohanaeze

Sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo reshen jihar Neja, Cif Valentine Oparaocha, wanda ya yi magana da jaridar Punch a ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta a garin Minna, ya nanata cewar majalisar Bago ba za ta cika ba idan babu dan Igbo koda daya ne a ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Oparaocha ya ce:

"Babu wani yanki na jihar da ba za ka ga dan kabilar Igbo namiji ko mace ba. Ka je kowace kasuwa, za ka gansu suna iya bakin kokarinsu sannan suna bayar da gudunmawarsu ga tattalin arzikin jihar, wannan ne dalilin da yasa muke ganin ba laifi bane don mun nemi a saka mu a majalisar.
"Yan kabilar Igbo mutane ne da suka dabi'antu da kasuwanci kuma suna bayar da gudunmawa fiye da sauran dabi'u wajen ci gaban jihar Neja, musamman wajen tattara kudaden shiga, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen aikata haka.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida Ya Ce Ya Na Bukatar Biliyan 6 Don Wadatar Da Makarantun Kano Da Kujerun Zama, Ya Koka Da Mulkin Ganduje

"Mun zabi Bago saboda danmu, Georfe Dike, ya bamu tabbacin gaskiyarsa na tafioya da yan Igbo. Mun zabe shi a lokacin da aka mayar da mu saniyar ware a kason da aka raba da sauran kabilu 26 da ba ‘yan asalin jihar ba.”

Matasan Igbo na yin Bago dari bisa dari

Oparaocha ya kara da cewa matasan kabilar Igbo a jihar Neja na goyon bayan Bago a kodayaushe.

Ya kara da cewar:

“Sun ce mu zabe shi domin ba zai bata mana rai ba kuma mun yi. Muna son gwamna ya yi mana kamar yadda ake yi a wasu jihohi ta hanyar shigar da mu cikin hukumar tsaro da majalisar zartarwa ta jihar."

Shugaban APC a jihar Neja ya yi murabus daga kujerarsa

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Haliru Zakari Jikantoro, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Shugaban jam'iyyar na APC ya yanke shawarar ne a bainar jama'a ba tare da bayyana wani dalili ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng