Fani-Kayode Ya Yi Magana Bayan Rashin Ganin Sunansa a Ministoci, Ya Fadi Mataki Na Gaba
- An fara maida martani kan rukuni na biyu na sunayen ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ayyana jerin ministocin da shugaban ƙasa ya naɗa a matsayin zaɓi na gari
- Haka nan kuma, Festus Keyamo, tsohon ministan kwadugo ya yaba da ministocin duk da ba bu sunansa a ciki
Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma makusancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Femi Fani-Kayode, ya yi magana kan ministocin da aka naɗa zuwa yanzu.
FFK ya bayyana gamsuwarsa da rukuni na biyu na sunayen ministocin da shugaba Tinubu ya miƙa wa majalisar dattawan Najeriya ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023.
Fani Kayode a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya taya sabbin Ministocin murnan naɗin da aka musu, yana mai bayyana su da zaɓi mafi nagarta.
Ya rubuta cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ina taya dukkan wadanda ke cikin jerin sunayen ministoci na farko da na biyu na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, murna."
"Dukkan su zabi ne masu kyau, kuma ina yi musu fatan alheri a hidimar al'ummar mu da zasu tasa a gaba."
"Na yi Minista shekaru 16 da suka wuce, kuma na san yadda matsayin ke tattare da kalubale."
Ya kuma bukaci masu kyakkyawar niyya da su yi musu addu’a yayin da suka ɗaura ɗamarar bauta wa kasa da kare muradun ‘yan kasa.
Keyamo ya goyi bayan waɗanda Tinubu ya naɗa a rukuni na biyu
Hakazalika, tsohon ministan kwadago, Festus Keyamo, ya ce ya ji dadin jerin sunayen ministoci na biyu da shugaba Tinubu ya tura majalisar dattawa.
A shafinsa na Tuwita, Keyamo ya ce:
"Kashi na biyu na sunayen ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya nada, zabi ne masu kyau. Ina taya su murna. Da fatan Allah ya yi musu jagora a ayyukansu daban-daban."
"Mun Shirya Zama Masu Shara a Villa" Miyetti Allah Ta Roki Tinubu Muƙamai
A wani labarin kuma Ƙungiyar Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN) ta roƙi shugaban ƙasa Tinubu ya waigo kan 'ya'yanta ya naɗa su muƙamai.
'Ya'yan ƙungiyar MACBAN sun bayyana cewa a shirye su ke su yi aiki a matsayin masu shara a fadar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng