Abdullahi Ganduje: Abubuwan Sani 7 Dangane Da Sabon Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa

Abdullahi Ganduje: Abubuwan Sani 7 Dangane Da Sabon Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis, 3 ga watan Agustan 2023, ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hakan na zuwa ne bayan kwamitin majalisar zartaswa na ƙasa na jam'iyyar, ya tabbatar da shi a taron da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton The Punch.

Abubuwan sani dangane da Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa Hoto: Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Muhimman abubuwan Sani 7 dangane da Abdullahi Umar Ganduje

Ga abubuwan sani guda bakwai dangane da sabon shugaban na jam'iyyar APC.

1. An haifi Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 1949 a ƙauyen Ganduje cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Ya halarci jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a jihar Kaduna inda ya samu kwalin digiri kan ilmin kimiyya a shekarar 1975. A shekarar 1979 ya samu digirin digirgir a jam'iar Bayero dake Kano a kwas ɗin 'Applied Educational Psychology'.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Jiga-Jigan APC Sun Tona Asirin Wike, Sun Faɗi Dalilinsa Na Haɗe Wa da Shugaba Tinubu

Ganduje ya koma jami'ar Ahmadu Bello daga shekarar 1984 zuwa 1985 domin yin digirin digirgir kan kwas ɗin 'Public Administration', sannan daga bisani ya samu dakta a fannin 'Public Administration' daga jami'ar Ibadan a shekarar 1993.

3. Ganduje ya shiga jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) a jamhuriya ta biyu inda ya riƙe muƙamin mataimakin sakatare na jihar Kano daga shekarar 1979 zuwa 1980

4. Ya zama kwamishinan ma'aikatar ayyuka, gidaje da sufuri ta jihar Kano a shekarar 1994.

5. A shekarar 1998, ya shiga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) inda ya nemi zama ɗan takarar jam'iyyar na gwamnan Kano amma ya yi rashin nasara a hannun Rabiu Musa Kwankwaso. Daga baya ya koma jam'iyyar APC tare da Kwankwaso a shekarar 2014.

6. Ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar Kano a lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso yake gwamna daga shekarar 1999 zuwa 2003 da shekarar 2011 zuwa 2015.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Shugabannin Jam'iyyar APC Na Kasa Da Suka Fito Daga Arewacin Najeriya

7. Ya maye gurbin Kwankwaso a matsayin gwamnan jihar Kano a shekarar 2015 sannan ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar a karo na biyu a shekarar 2015.

'Yan Arewa Da Suka Taba Shugabancin APC

A wani labarin kuma, mun kawo mu ku ƴan yankin Arewacin Najeriya da suka taɓa riƙe shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya zama sabon shugaban jam'iyyar a ranar Alhamis 3 ga watan Yuli ya bi sahun mutum uku da suka fito daga Arewacin Najeriya da suka taɓa riƙe shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng