Dirama a Majalisa Yayin da Ministar da Tinubu Ya Nada Ta Kauce Wa Tambaya Kan Mijinta

Dirama a Majalisa Yayin da Ministar da Tinubu Ya Nada Ta Kauce Wa Tambaya Kan Mijinta

  • Majalisar dattawan Najeriya na ci gaba da aikin tantance sunayen mutanen da shugaba Tinubu ya aike mata a matsayin ministoci
  • Sai dai an yi wata dirama yayin tantance Minista mace daga jihar Imo, Doris Uzoka, wacce ta kauce wa amsa tambaya kan mijinta
  • Sanata Akpabio ya yi mata tambayoyi kan iyalinta amma yayin amsawa sai ta tsallake zancen miji, sanatoci suka kama dariya

FCT Abuja - An yi wata 'yar dirama a majalisar dattawa ranar Larabar yayin da Dakta Doris Uzoka, daya daga cikin wadanda shugaba Bola Tinubu ya nada a matsayin ministoci, ta tsallake wata tambaya kan mijinta.

Daily trust ta ce da farko dai Uzoka wadda ‘yar asalin jihar Imo ce ta fara gabatar da kanta inda ta zayyana wasu daga cikin abubuwan da ta cimma nasara a rayuwarta.

Kara karanta wannan

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

Dakta Doris Uzoka yayin amsa tambayoyi a majalisar dattawa.
Dirama a Majalisa Yayin da Ministar da Tinubu Ya Nada Ta Kauce Wa Tambaya Kan Mijinta Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Likitan wacce daga baya ta koma ma’aikaciyar banki ta dauki lokaci kafin amsa tambayoyin da aka jefa ta, amma da aka tambaye ta game da danginta, sai ta wayance ta tsallake tambayar.

Yadda Sanatoci suka titsiye ta da tambayoyi

Sanatoci uku sun yi mata tambayoyi kan yadda ta gudanar da ayyukanta na baya da kuma abin da za ta yi daban idan majalisa ta amince da naɗinta a matsayin minista.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bisa sa'a sai shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙi karɓan rokon wasu sanatoci na ta risina kawai ta wuce, ya ce dole ta amsa tambayoyin da aka mata.

Bugu da ƙari, Sanata Akpabio ya gaya wa sauran sanatocin cewa shi kansa yana da tambayoyin da zai mata bayan ta amsa waɗannan, rahoton Naija News ya tattaro.

Shugaban majalisar dattawan ya ce:

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Babban Dalilin da Ya Sa Majalisar Dattawa Ba Ta Tsitsiye Wike Ba Ya Bayyana

“Ba na tsammanin CV dinta ya cika, ina tunanin wasu shafuka sun ɓace saboda ban ga komai game da rayuwar iyali ba. Sunan mahaifinta, mahaifiyarta, sunan mijinki, da 'ya'yanki nawa."

Yadda ta kauce wa faɗin sunan mijinta

Yayin amsa waɗannan tambayoyi, Doris Uzoka ta ce:

"Bari na fara da tambayar ƙarshe, Mista da Misis Uzoka ne suka haife ni, ina da 'ya'ya da yawa, wasu ni na haife su wasu kuma ba ni na haife su ba, ina ɗaukar ɗawainiyar mutane da yawa, maza da mata."

Daga nan sai Sanatoci suka kece da dariya yayin da ministar ta yi murmushi ta tsallaka zuwa amsa wasu tambayoyin, ta kauce wa bada amsa kan mijinta.

Jerin Sunayen Jihohin Haihuwa Na Ƙarin Ministoci 19 da Tinubu Ya Mika Majalisa

A wani labarin kuma Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu , ya miƙa ƙarin ministoci 19 ga majalisar dattawa ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Rikici Yayin Da Wata Mai Koyon Sana’a Ta Tsere Da Jinjirin Uwar Dakinta Dan Kimanin Watanni 2 A Wurin Biki, An Bazama Nemanta

Mun haɗa maku sunayen ragowar ministoci 19 baki ɗaya tare da sunan jihohim da aka haifi kowane ɗaya daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262