Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Karar da Atiku Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Karar da Atiku Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

  • Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa ta fara shirye-shiryen yankr hukunci kan zaben da shugaba Tinubu ya lashe a 2023
  • A zaman ranar Talata, Kotun ta aje hukunci kan karar da Atiku ya shigar, ta ce zata sanar da ranar yanke hukunci nan ba da jima wa ba
  • Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP yana kalulantar nasarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC

FCT Abuja - Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben shugaban kasa a Najeriya ta fara haramar yanke hukunci kan babban zaben da Bola Tinubu ya samu nasara a 2023.

Daily Trust ta tattaro cewa Kotun ta jingine yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ƙalubalanci nasarar Tinubu.

Kotun zaɓe na shirin yanke hukunci kan nasarar Tinubu.
Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Karar da Atiku Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Kwamitin alƙalai 5 da ke sauraron ƙarar karkashin jagorancin mai shari'a Haruna Tsammani ya ce nan ba da jimawa ba kotu zata sanar da ranar yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: NSA Na Shugaba Tinubu Ya Sa Labule Da Gwamnoni 5 a Abuja, Sahihan Bayanai Sun Fito

Tun da farko dai kotun ta karɓi rubutaccen jawabi na karshe daga kowane ɓangare a karar da ta ƙalubalanci nasarar shugaba Bola Tinubu, dan takara a inuwar APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alhaji Atiku, mataimakin shugaban ƙasa a tsakanin 1999 zuwa 2007, ya halarci zaman Kotu na yau Talata a Abuja, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Yadda shari'ar ta samo asali

Idan baku manta ba hukumar zabe ta ƙasa INEC ta gudanar da zaben shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Bayan kammala tattara sakamako, shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wannda ya lashe zaɓen da kuri'u mafi rinjaye.

Bisa rashin gamsuwa da sakamakon zaɓe, Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP suka shigar da ƙara gaban kotun sauraron kararrakin zaɓe mai zama a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

“Bata Lokaci Da Yaudara Ne Kawai”: Atiku Ya Caccaki Jawabin Shugaba Bola Tinubu

Atiku ya roƙi Kotun da ta soke nasarar Bola Tinubu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu kuma ta ayyana shi a matsayin sahihin wanda ya samu nasara.

NSA Na Shugaba Tinubu Ya Sa Labule Da Gwamnoni 5 a Abuja, Sahihan Bayanai Sun Fito

A wani rahoton kun ji cewa Nuhu Ribadu, mai ba shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro ya gana da gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas a Abuja.

Ba bu wata sanarwa a hukumance kan maƙasudin wannan taro na sirri amma ana ganin ba zai rasa alaƙa da tabarbarewar tsaro ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262