Jawabin Tinubu Bata Lokaci Da Yaudara Ne Kawai, Atiku Ya Caccaki Shugaban Kasa

Jawabin Tinubu Bata Lokaci Da Yaudara Ne Kawai, Atiku Ya Caccaki Shugaban Kasa

  • Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki jawaban da Tinubu ya yi ranar Litinin
  • Ya ce jawaban na shugaba Tinubu cike suke da tsantsar yaudara da kuma ɓata lokaci
  • Atiku ya kuma ce Tinubu ya yi jawaban ne kawai don ya hana ƙungiyar 'yan ƙwadago gudanar da zanga-zangar da suke shirin aiwatarwa

FCT, Abuja - Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jawaban da Shugaba Tinubu ya yi yaudara ce da kuma bata lokaci.

Mai taimakawa Atiku a harkokin yaɗa labarai Phrank Shaibu ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala jawabin na Tinubu ranar Litinin, 31 ga watan Yuli.

Ya ce Tinubu ya yi jawabin ne don kawai ya gamsar da ƙungiyoyin 'yan ƙwadago kan su dakatar da zanga-zangar da suka ƙudiri aniyar gabatarwa a cikin makon nan.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sanar da Sabuwar Garaɓasa Ga Ɗaliban Najeriya

Atiku ya caccaki jawaban Tinubu
Atiku ya ce babu komai a cikin jawaban Tinubu sai yaudara da ɓata lokaci. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku ya ce Tinubu ya yi adawa da cire tallafin man fetur a baya

Ya kuma jaddada cewa jawabin na Tinubu na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur ba tare da yin wani tsari da zai hana mutane ci gaba da shan wuya ba wacce suke a cikinta tun lokacin da APC ta fara mulki a 2015.

Ya ƙara da cewa maimakon Tinubu ya bai wa mutane haƙuri kan halin da ya jefa su a ciki, ya ɓuge da ɗora laifin wahalhalun da ake sha a kan masu cuwa-cuwa kan tallafin man fetur.

Ya kuma ce maganar Tinubu ta cewa shi ɗan goyon bayan cire tallafin man fetur ne ba gaskiya ba ne, inda ya ce Shugaban ya yi adawa da Jonathan a lokacin da ya cire tallafin a shekarar 2012 in ji rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi Ga 'Yan Najeriya, Bayanai Sun Fito

Atiku ya caccaki tsarin bayar da jarin naira 50,000 ga ƙananan 'yan kasuwa

Shaibu ya kuma ce batun tsarin naira 50,000 da Tinubu ya ce zai bai wa ƙananan 'yan kasuwa ba zai tasiri ba saboda tsadar rayuwa, matsalar canjin kuɗaɗe da kuma cin hanci da rashawa.

Ya ce tsarin bada naira 50,000 ɗin da Tinubu yake shirin yi, ya yi kama da tsarin Trader moni da gwamnatin baya ta zo da shi, wanda bai tsinanawa kowa komai ba in banda wasu tsirarun da suka tattare kuɗaɗen zuwa lalitarsu.

Ya ce Tinubu bai yi wani tsari ba ta yadda talaka zai amfana, inda ya bayyana hakan a matsayin yaudara wacce kowa zai shaida hakan nan ba da jimawa ba kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Shaibu ya kuma ƙalubalanci Tinubu kan yadda zai bai wa manoma hektoci 500,000 na ƙasa domin bunƙasa noma, inda ya ce manyan jihohin da ke samar da amfanin gona na fama da matsananciyar matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri Da Matasan Jam'iyyar APC Kan Batun Ministoci

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta tara sama da tiriliyan ɗaya tun bayan cire tallafi

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan iƙirarin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, na cewa gwamnatinsa ta tara sama da naira tiriliyan ɗaya tun bayan cire tallafin man fetur.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi na kai tsaye ga 'yan ƙasa a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng