Majalisar Dattawa Ta Kammala Tantance Ministocin Tinubu 20 A Abuja
FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta tantance ministoci 20 a yau Litinin 31 ga watan Yuli a majalisar da ke Abuja.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Majalisar ta fara tantance ministocin ne da Shugaba Bola Tinubu ya mika mata a makon da ya gabata.
Ministocin da aka zaba sun fito daga jihohi 25 da suka hada da tsoffin gwamnoni hudu da tsoffin ‘yan majalisun Tarayya shida da kuma mata guda bakwai, cewar Premium Times.
Yadda aka tantance ministocin a majalisar
Daga cikin jerin ministocin 28, an tantance guda 20 a yau bayan majalisar ta fara tantance su a dakin majalisar da ke Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng ta tattaro cewa 20 daga cikin 28 sun kammala gyara takardunsu a majalisar a yau Litinin 31 ga watan Yuli.
Rahotanni sun tabbatar cewa wadanda ba su kammala gyara takardun nasu ba a yau, ba sa kasar Najeriya, cewar gidan talabijin na Channels.
Jerin wadanda suke a majalisar a yau yayin tantancewar:
1. Sanata Abubakar Kyari - Borno
2. Abubakar Eshiokpekha Momoh - Edo
3. Nyesom Ezenwo Wike - Rivers State
4. Injiniya Farfes Joseph Terlumun Utsev - Benue
5. Sanata John Owan Enoh - Cross River
6. Barista Bello Muhammad - Sokoto
7. Mohammed Badaru Abubakar -Jigawa
8. Ambasada Yusuf Maitama Tuggar- Bauchi
9. Sanata. Abubakar Sani Danladi -Taraba
10. Barista Uju-Ken Ohaneye - Anambra
11. Dakta Olubunmi Tunji-Ojo - Ondo
12. Dakta Betta Edu - Cross River
13. Iman Sulaiman Ibrahim- Nasarawa
14. Injiniya Ahmed Musa Dangiwa - Katsina
15. Cif Uche Geoffrey Nnaji - Enugu
16. Stella Erhuvwuoghene Okotete - Delta
17. Sanata Allwell Onyesoh
18. Sanata Tokunbo Abiru
Yayin tantancewar an samu hatsaniya bayan minista daga jihar Benue ya fadi shekarunsa inda Sanata Tokunbo Aburi daga jihar Lagos ya kalubalance shi da ya yi bayani akai.
Farfesa Joseph Utsev ya bayyana cewa an haifeshi a shekarar 1980 kuma ya kammala sakandare a 1989, yayin da Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa ya kare shi da cewa shima ya na da irin wannan matsalar.
Ministocin Tinubu: Abinda Ya Sa Bamu Titsiye Wike Ba, In Ji Akpabio
A wani labarin, shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana dalilin da yasa ba su titsiye Nyesom Wike ba a majalisa lokacin tantance shi.
Akpabio ya umarci Wike da ya risina ya wuce bayan ya karanto takaitaccen tarihinsa yayin tantance shi a majalisa.
Asali: Legit.ng