Ministocin Tinubu: Abinda Ya Sa Bamu Titsiye Wike da Tambayoyi Ba, Akpabio
- Sanata Godswill Akpabio ya yi ƙarin haske kan abinda ya sa majalisa ba ta titsiye tsohon gwamnan jihar Ribas da tambayoyi ba
- Nyesom Wike bai sha wahala ba yayin da ya bayyana a gaban majalisar dattawa domin tantance shi a matsayin minista
- Akpabio ya ce sun umarci Wike ya risina kawai ya ƙara gaba saboda ya taɓa rike kujerar Minista a shekarun da suka gabata
FCT Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana dalilin da ya sa ba a tsitsiye tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da tambayoyi ba yayin tantance shi.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa majalisa ta umarci Wike ya risina ya wuce bayan ya gama karanta taƙaitaccen tarihinsa da kuma amince wa da buƙatar Sanata Barinada Mpigi (PDP, Ribas).
Majalisa Ta Dauki Matsaya Kan Ministan Da Ya Shiga Jami'a Bayan Ya Ci Darussa 2 a Jarabawar Sakandire
Duk da kasancewarsa ɗan jam'iyyar adawa, meyasa Sanatoci ba su tsitsiye shi ba?
Da yake tsokaci bayan kammala tantance tsohon gwamnan, Sanata Akpabio ya ce ba su tasa Wike da tsauraran tambayoyi ba saboda majalisar dattawa tana da bayanansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Sanatocin ya bayyana cewa sun umarci Wike ya risina ya tafi ne saboda akwai cikakken bayanansa a majalisa kasancewar ya taɓa riƙe kujerar minista a baya.
Ya ƙara da cewa Wike ya taɓa kawo kansa gaban majalisar dattawa kuma an tantance shi a lokacin da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya naɗa shi minista.
"Sakamakon an taɓa naɗa shi a matsayin minista, ba bu dalilin da zai sa mu titsiye shi da tambayoyi masu yawa," inji Sanata Akpbaio.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Wike ya riƙe kujerar ƙaramin ministan ilimi a lokacin Jonathan, bisa haka majalisa ta umarci ya risina mata kawai ya ƙara gaba.
"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa
Majalisar dattawa ta fara aikin tantance ministoci 28 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya turo mata tun ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023.
Takaddama Ta Barke a Majalisa Kan Shekarun Ministan Shugaba Tinubu
A wani rahoton na daban kun ji cewa Taƙaddama ta ɓarke a majlisar dattawan Najeriya kan bayanan shekarun Farfesa Joseph Turlumum, ɗaya daga cikin ministoci 28.
Farfesa Farfesa Joseph Turlumum ɗan asalin jihar Benuwai ne da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Asali: Legit.ng