Hotunan Ganduje Sun Kai Hedikwata, Tsohon Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar APC

Hotunan Ganduje Sun Kai Hedikwata, Tsohon Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar APC

  • A hedikwatar APC a Abuja, hotunan Abdullahi Umar Ganduje ne su ke yi wa mutum maraba da zuwa
  • Magoya bayan tsohon Gwamnan Kano sun ce shi ne zai iya dunkule ‘ya ‘yan jam’iyyar ta APC a Najeriya
  • Sunanan Abdullahi Ganduje ne yake yawo a matsayin wanda zai zama sabon shugaban jam’iyya na kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A karshen makon jiya ne aka ga hotunan Abdullahi Umar Ganduje a hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa da ke babban birnin tarayya na Abuja.

The Cable ta ce allon da yake dauke da hoton shugaban kasa da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce tsohon gwamnan zai iya rike jagorancin APC.

Hoton tsohon Gwamnan yake yi wa jama’a maraba da zuwa babban ofishin jam’iyyar, ba a maganar Sanata Tanko Al-Makura ko Boss Mustapha.

Kara karanta wannan

PDP da daukar aiki? Jama'a sun yi mamaki yayin da PDP ta ce za ta dauki aiki mai girma

Shugaban APC
APC: Abdullahi Ganduje da Abdullahi Adamu Hoto: Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Kwanaki da tafiyar Abdullahi Adamu, sai aka ji masu tallata Ganduje su na cewa shi ne zai iya hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyya APC a fadin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ganduje ne wanda ya cancanta da zai hada-kan jam’iyya mai mulki saboda kalubale nan gaba.”

- Magoya baya

Za a ga hoton Ganduje yana dauke da hular ‘Asiwaju’, allon ya ce shugaban yana bakin kokari dare da rana domin farfado da tattalin arzikin kasa.

Hedikwatar APC da ke rike da mulki tun Mayun 2015 na kan titin Blantyre a Wuse 2.

Shugabannin APC a tarihi

A cikin shugabannin APC da aka yi a tarihi, John Odigie Oyegun ne ya fi kowa dadewa, duk da shi ma bai gama wa’adinsa yadda ya so ba.

Adams Oshiomhole kuwa ya bar jam’iyyar ne bayan kusan shekaru biyu, aka maye gurbinsa da kwamitin rikon kwarya na su Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

Dalilan da Suka Jawo Babu Minista ko 1 Daga Kano, Filato da Legas a Sahun Farko

Da karfi da yaji aka tilastawa Gwamna Mai Mala Buni shirya zaben da ya kawo majalisar Abdullahi Adamu wanda ya shiga ofis a 2022.

Shugaban rikon kwarya ne ko kuwa?

Vanguard ta rahoto wasu dattawan APC su na cewa Abdullahi Ganduje zai zama shugaban rikon kwarya ne, daga nan sai a shirya zabe na kasa.

Janar Lawrence Onoja mai ritaya ya ce APC za ta duba yankin da ya dace a kai kujerar, a zabe za a fito da shugaban da zai ja ragamar jam’iyya.

Dattawan sun kunshi Cesnabmihilo Dorothy Nuhu-Aken’Ova; Musa Mwanti Bwari; Ishaya R. Pam; Mathias Terwase Byuan; da irinsu Joseph Azi.

...Uban Abba su ke da jam'iyya

Zuwa yanzu Sanata Abdullahi Adamu ya zama tarihi a majalisar NWC, magana tayi karfi sosai a kan maye gurbin shi da tsohon Gwamnan Kano.

Wasu ‘Yan Arewa sun ce babu wanda ya dace ya rike APC illa Dr. Ganduje, a halin da ake ciki an ji labari alamu sun nuna babu wanda yake ja da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng