Kotu Ta Hana Ministan Da Tinubu Ya Zabo Daga Rike Mukami? Lauya Ya Yi Martani

Kotu Ta Hana Ministan Da Tinubu Ya Zabo Daga Rike Mukami? Lauya Ya Yi Martani

  • Lauyan Sanata Sani Danladi, Ujah Ujah ya yi watsi da rahoton cewa kotun ƙoli ta hana wanda yake karewa daga riƙe wani muƙami har na tsawon shekara 10
  • Ujah ya bayyana cewa rahotannin soki burutsu ne kawai wanda wasu ƴan siyasa a jihar Taraba suka yaɗa wa
  • Danladi yana daga cikin ministoci 28 da Shugaba Tinubu ya aike da sunayensu ga majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli domin tantancewa da amincewa da su

Ujah Ujah, lauyan Sanata Sani Danladi, ɗaya daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu ya zaɓo, ya yi martani kan rahoton cewa a shekarar 2019 kotun ƙoli ta hana wanda yake karewa yin takara ko riƙe wani muƙami har na shekara 10 bisa yin amfani da takardun bogi.

Ujah ya bayyana cewa babu wani umarnin kotu da ya hana Danladi riƙe muƙami, inda ya ƙara da cewa jita-jitar wasu ƴan siyasa ne daga jihar Taraba kawai su ke yaɗa ta, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon 'Yar Najeriya Mai Tallar Ruwa Bayan Ta Koma Turai Ya Janyo Cece-Kuce a Yanar Gizo

Kotu ta hana ministan Tinubu rike mukami
Lauya ya ce kotu ba ta hana Danladi rike mukami ba Hoto: Hon Aliyu Usman
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli, inda ya ce Danladi ya sauke nauyin dake kansa ba tare da wani tarihin laifi a tattare da shi ba, lokacin da yake riƙe da muƙamai.

"Soki burutsu ne kawai domin babu wata hujja ko umarnin kotu da ya kama Sanata Sani Abubakar Danladi da laifi." A cewarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta wanke Sanata Sani Danladi

Ya yi bayanin cewa Danladi ya shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya a Jalingo domin ta yi fatali da hukuncin farko kan ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar da shi, saboda kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar.

Lauyan ya bayyana cewa kotun ta amince da buƙatar Danladi a ranar 15 ga watan Oktoban 2021, inda ya shafe hukuncin da ta yi a baya.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya 'Yan Bindiga Suka Kwamushe Ni, Babban Boka Ya Yi Bayani Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci

Lauyan na Danladi ya bayyana cewa rashin gamsuwa da hukuncin na kotun, jam'iyyar PDP ta ɗaukaka ƙara wacce kotun ɗaukaka ƙara ta yi fatali da ita a ranar 23 ga watan Janairun 2023.

Peter Obi Ya Magantu Kan Takaddamar Jami'an DSS Da NCoS

Rahoto ya zo cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi martani kan taƙaddamar da jami'an DSS da na NCoS suka yi a kotu kan Godwin Emefiele.

Peter Obi ya bayyana abinda jami'an suka yi a matsayin abun kunya wanda ya zubar da ƙimar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng