Matasan APC da Mata Sun Roki Tinubu Ya Zabi Boss Mustapha a Matsayin Shugaban APC

Matasan APC da Mata Sun Roki Tinubu Ya Zabi Boss Mustapha a Matsayin Shugaban APC

  • Matasa da matan jam'iyyar APC sun jingine Ganduje, sun roki shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya zaɓi wanda suke so ya shugabanci jam'iyya
  • A wani taron manema labarai a Kaduna, ƙungiyar matasa da matan ta ayyana goyon baya ga tsohon SGF, Boss Mustapha
  • A cewarsu, a halin da APC ta tsinci kanta, tana bukayar gogaggun mutane da suka san harkar shugabanci kamar Mustapha

Kungiyar Matasa da Mata ta APC ta bayyana goyon bayanta ga tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha a matsayin wanda ya cancanci zama shugaban jam’iyyar na kasa.

Wakilan ƙungiyar, Jibril Adamu Seze da Kwamaret Nuhu Sani ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai da suka kira a Kaduna, kamar yadda rahoton Leadership ya tattaro.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.
Matasan APC da Mata Sun Roki Tinubu Ya Zabi Boss Mustapha a Matsayin Shugaban APC Hoto: leadership
Asali: UGC

A cewarsu, idan har ana son kawo kudirori na gari, kirkire-kirkire, dabarar siyasa da ci gaban da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke fatan samar wa yan Najeriya, Boss Mustapha ne mutumin da zai yi wannan aiki.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: An Faɗi Sunan Wanda NEC Ke Shirin Naɗa Wa a Matsayin Shugaban APC Na Ƙasa Ranar Alhamis

Kungiyar ta ci gaba da cewa, irin wannan gagarumin aiki na shugabancin APC yana bukatar ilimi, iya aiki da gogewar gogaggen shugaban al’umma kamar Mustapha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ƙungiyar ta ce:

“Ko shakka babu jam’iyyarmu mai daraja APC tana cikin wani mummunan hali bayan murabus din shugabanta na kasa da sakatare, da mataimakin shugaba na yankin Arewa maso Yamma."
"Hakan ya nuna cewa APC na bukatar wanda ya fahimci yadda za a gyara jam’iyyar tare da dawo da ita kan turbar samun ci gaba mai dorewa a siyasance."
"Haka zalika a halin yanzu APC tana buƙatar mutum mai hikima wanda ya san yadda zai bullo da hanyoyin tallafa wa shugaban ƙaa, Bola Tinubu ya cimma burinsa na sabunta fatan yan Najeriya."

Matasa da mata sun bayyana wanda ya dace da shugabancin APC

Bayan haka, mata da matasan APC suka yi kira ga shugaba Tinubu ya duba buƙatarsu, ya amince da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a matsayin shugaban APC na gaba.

Kara karanta wannan

Hanya Ta Buɗe: Ganduje Ya Ƙara Samun Gagarumin Goyon Bayan Zama Shugaban APC, Bayanai Sun Fito

"Muna kira ga shugaban kasa da ya yi la'akari da bukatarmu, ya duba sannan ya zabi tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a matsayin shugaban jam'iyyarmu na kasa."

Tsofaffi 4 Sun Samu Shiga Jerin Kwamishinoni 17 da Gwamnan Gombe Ya Mika Majalisa

A wani rahoton kuma Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya miƙa sunayen kwamishinoni 17 ga majalisar dokokin jihar Gombe ranar Jumu'a.

Tsoffin kwamishinoni 4 da suka yi aiki a zangon mulkin farko ne kaɗai suka samu shiga jerin sunayen mutum 17.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262