Tsofaffi 4 Sun Samu Shiga Jerin Kwamishinoni 17 da Gwamnan Gombe Ya Mika Majalisa

Tsofaffi 4 Sun Samu Shiga Jerin Kwamishinoni 17 da Gwamnan Gombe Ya Mika Majalisa

  • Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya miƙa sunayen kwamishinoni 17 ga majalisar dokokin jihar Gombe ranar Jumu'a
  • Tsoffin kwamishinoni 4 da suka yi aiki a zangon mulkin farko ne kaɗai suka samu shiga jerin sunayen mutum 17
  • Inuwa Yahaya ya miƙa sunayen ga majalisa bayan cikar kwana 60 da hawansa mulki kamar yadda kundin mulki ya tanada

Gombe - Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da jerin sunayen mutane 17 da ya nada a matsayin kwamishinoni ga majalisar dokokin jihar domin tantance wa.

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya mika jerin sunayen mutanen ga magatakardar majalisar dokokin jihar, Barista Rukaiyatu A. Jalo.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe.
Tsofaffi 4 Sun Samu Shiga Jerin Kwamishinoni 17 da Gwamnan Gombe Ya Mika Majalisa Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsoffin kwamishinoni 4 da suka yi aiki da gwamnan a zangon mulkinsa na farko sun samu nasarar koma wa a zango na biyu.

Kara karanta wannan

An Nada Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ekweremadu, a Matsayin Kwamishina

Tsofaffin kwamishinonin da suka sake komawa su ne, Dakta Habu Dahiru, Barista Zubairu Mohammed Umar, Dakta Aishatu Umar Maigari da kuma Muhammad Gambo Magaji.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Yahaya ya mika jerin sunayen ne kwanaki 60 cif da rantsar da shi a karo na biyu, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, Leadership ta tattaro.

Idan zaku iya tunawa, wata doka da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaɓa wa hannu, ta umarci shugaban ƙasa da gwamnoni su naɗa mambobin majalisarsu cikin kwana 60 na farko da hawa mulki.

Jerin sunayen kwamishinoni 17 da gwamna Yahaya ya naɗa

Mun tattaro muku jerin sunayen kwamishinoni 17 da gwamna Yahaya ya aike wa majalisa da kuma kananan hukumomin da suka fito. Ga su kamar haka:

1. Dakta Habu Dahiru (Yamaltu/Deba)

2. Barista Zubairu Mohammed Umar (Funakaye)

3. Dakta Aishatu Umar Maigari

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Aliyu Ya Miƙa Sunayen Sabbin Kwamishinoni 16 Ga Majalisar Dokoki

4. Muhammad Gambo Magaji (Dukku)

5. Mohammed Waziri (Akko LGA)

6. Adamu Inuwa Pantami (Gombe)

7. Mijinyawa Ardo Tilde (Funakaye)

8. Mohammed Shetima Gadam (Kwami)

9. Asma’u Iganus (Shongom)

10. Mohammed Saidu Fawu (Billiri)

11. Salihu Baba Alkali (Nafada)

12. Alhaji Nasiru Mohammed Aliyu (Yamaltu/Deba)

13. Dakta Barnabas Malle (Kaltungo)

14. Dakta Usman Maijama’a Kallamu (Kwami)

15. Laftanar Kanal Abdullahi Bello mai ritaya (Balanga)

16. Sanusi Ahmed Maidala (Akko)

17. Dakta Abdullahi Bappah Garkuwa (Gombe).

Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranakun Gudanar da Manyan Taruka Guda 2

A wani labarin kuma Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa ya sanya ranakun gudanar da taron shugabanni da na majaliaar zartarwa (NEC).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a a Abuja mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa, Barista Festus Fuanter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262