Orji Kalu Ya Bayyana Yadda Ya Ki Amincewa da Nadin Ministan Tinubu, Ya Fadi Dalili
- Sanata Orji Kalu ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya masa tayin zama mamban majalisar zartarwa amma ya ƙi amince wa da tayin
- Ya ce fadar shugaban ƙasa ta tunkare shi da wannan tayin mai gwaɓi jim kaɗan bayan ya janye daga takarar shugaban majalisar dattawa
- Kalu ya bayyana cewa shi da kansa ya faɗa wa Tinubu ya zaɓi duk wanda ya ga dama daga jihar Abiya
Tsohon dan takarar shugaban majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana yadda ya ki amince wa da tayin zama minista.
A wani faifan bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi, Kalu ya ce gwamnatin tarayya ta tuntube shi domin ya kasance cikin majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu.
Sanata Kalu ya ƙi amincewa da tayin, kuma ya bukaci shugaban kasar da ya zabi duk wanda yake so daga jihar Abia.
A kalamansa, Kalu ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lokacin da na hakura da takarar shugabancin majalisar dattawa, gwamnatin tarayya ta so na zama minista... na roke shi (Shugaba Bola Tinubu) ya sanya duk wanda yake so."
Wa Tinubu ya zaɓo daga jihar Abia?
A halin yanzu, Nkiru Onyejeocha, mambar majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Isuikwuato/Umunneochi daga jihar Abia, ita ce shugaba Tinubu ya ɗauƙo daga Abia.
Onyejiocha na daya daga cikin jiga-jigan mambobi a majalisar dokokin kasar nan, saboda tun a shekarar 2007 take a majalisa.
A shekarar 2019, Onyejocha ta tsaya takarar shugaban majalisar wakilan tarayyar Najeriya wacce maza ke da rinjaye, inda ta fafata da Femi Gbajabiamila daga jihar Legas.
Babban batun da ta yi yakin neman zabe shi ne a miƙa kujerar kakakin majalisa zuwa yankinta (Kudu maso Gabas) don samun daidaiton rabon manyan madafun iko na tarayya tsakanin shiyyoyi shida.
Bayan Janye Masa Takara, Mace Ɗaya Tilo Da Ta Nemi Tikitin APC Ta Samu Babban Mulki a Gwamnatin Tinubu
Sai dai a ƙarshe, ta janye daga takara awanni 24 kacal gabanin fara zaɓen kakakin majalisar wakilan tarayya.
Fitaccen Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Nada Wike a Matsayin Minista
A wani rahoton kuma Gwamna Fubara ya taya magabacinsa, Nyesom Wike murnar shiga cikin jerin sunayen ministocin shugaba Tinubu.
Gwamnan Fubara na Ribas ya nuna kwarin guiwa da cancantar magabacinsa, yana mai cewa kokarinsa wajen haɗa kan ƙasa ne ya kai shi ga nasara.
Asali: Legit.ng