Hanya Ta Budewa Abdullahi Ganduje Wajen Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC
- Tun da Abdullahi Adamu ya yi murabus, ana bukatar APC ta samu sabon shugaban jam’iyya
- Kungiyar wasu matasa daga Arewa maso tsakiya sun yi wa Dr. Abdullahi Umar Ganduje mubaya’a
- Shugabannin jam’iyyar ta APC sun nuna yankinsu ya sallama wannan kujera ga Arewa maso yamma
Abuja - Gungun shugabannin jam’iyyar APC na yankin Arewa maso tsakiya, sun yarda Abdullahi Umar Ganduje ya zama shugaba na kasa.
A karshen makon nan rahoto ya fito daga Punch cewa shugabannin APC na Arewa ta tsakiya sun gamsu Dr. Abdullahi Ganduje ya karbi jam’iyya.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban wannan tafiya, Okpokwu Ogenyi ya ce a shirye suke su bi bayan tsohon Gwamnan.
Mubaya'a ga Abdullahi Umar Ganduje
"Duk da yankinsu ya dace ya fito da shugaban jam’iyya na kasa, Mista Okpokwu Ogenyi ya nuna duk sun mika wuya ga Ganduje ya jagorance su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mu mutanen Arewa ta tsakiya mun rike shugabancin duka jam’iyyu masu mulki a kasar nan, kuma mun yi kokari ta fuskantar tafiyar da jam’iyya.
Mu na alfahari da cewa shugaban jam’iyya na kasa da ya jagoranci APC a zaben shugaban Najeriya na karshe da aka yi, daga yankinmu ya fito.
A yau babanmu wanda shi ne shugaban jam’iyya a da, ya yi murabus, babu wanda ke kujerar.
A dalilin haka, kun san ba a barin mukami haka kurum babu kowa, saboda haka ana bukatar kawo wanda ya dace domin tafiyar da jam’iyyar gaba.
- Okpokwu Ogenyi
Saura 'Yan Arewa maso gabas
Blueprint ta ce wanda ya dace kuwa ba kowa ba ne a wurin matasan illa Ganduje wanda ya yi gwamna a Kano, su ka ce ya kawo cigaba sosai.
Tsohon Gwamnan na Kano ya samu goyon bayan maye gurbin Abdullahi Adamu jim kadan bayan mubaya’ar shugabanni na Arewa maso yamma.
Yadda za a raba Ministocin tarayya
Ku na da labari cewa mu na hasashen Farfesa Muhammad Ali Pate da Farfesa Joseph Utsev za su iya zama Ministocin lafiya da harkokin ruwa.
Da alama Ahmad Dangiwa zai zama Ministan gidaje, sai Iman Ibrahim ta gaji Sadiya-Farouk, David Umahi kuma zai samu mukamai mai tsoka a FEC.
Asali: Legit.ng