Shugabancin APC: Bamu Yanke Waɗanda Za Su Cike Gurbi Ba, Felix Morka

Shugabancin APC: Bamu Yanke Waɗanda Za Su Cike Gurbi Ba, Felix Morka

  • Sakataren watsa labaran APC ta ƙasa, Felix Morka, ya ce har yanzun ba a cimma matsaya kan wanda zai maye gurbin Abdullahi Adamu ba
  • Kakakin APC ya ce batun Ganduje da ake ta yaɗa wa duk jita-jita ce amma ba bu wata sanarwa a hukumance
  • A cewarsa, suna fatan nan ba da jimawa ba NEC zata cike guraben da ke cikin kwamitin gudanarwa NWC

Kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana cewa har yanzun jam'iyya mai mulki ba ta cimma matsaya kan waɗanda zasu cike gurbin shugaba da sakatare na ƙasa ba.

Morka ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV cikin shirinsu mai taken Siyasa a yau ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023 da yamma.

Kakakin APC da tsohon gwamnan Kano, Ganduje.
Shugabancin APC: Bamu Yanke Waɗanda Zasu Cike Gurbi Ba, Felix Morka Hoto: punch, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ya ce rahoton da ke yawo cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Sanata Ajibola Basiru, su ne zasu hau kujerun shugaba da sakataren jam'iyya ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Sanata Mai Fada a Ji? Hadimin Gwamna Ya Bayyana Gaskiyar Zance

Ya kara da cewa jam’iyyar APC ba za ta tsaya ɓata lokaci wajen tantance bayanan da mhukuntanta ba su amince da su ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin APC ya ce:

"Har yanzun bamu cimma matsaya ba kan wannan batun mai muhimmanci amma kamar yadda na faɗa muna fatan majalisar zatarwan APC (NEC) ta yi abinda ya dace wajen maye gurbin shugabanni 2."
"Ba mu cikin masu yaɗa hasashe har sai ya fito a hukumance, ba mu tabbatar da shi ba; ba mu fito don tantance bayanan da hukumomin jam’iyyar ba su tattauna ba kuma ba su amince da su ba."

Yaushe APC zata sanar da sabon shugaban jam'iyya da sakatare?

Da aka tambaye shi kan yaushe jam'iyya mai mulki zata sanar da waɗanda zasu cike gurbin shugaban APC na ƙasa da Sakatare, Felix Morka ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka

"Ina fatan nan bada jimawa ba za a yi komai a gama. Muna tsammanin NEC zata tattauna batun guraben da babu kowa a kwamitin gudanarwa NWC lokacin taro mai zuwa."

"Zasu Iya Aiki a Ko Ina" Gbaja Ya Yi Bayanin Kan Ma'aikatun Ministocin Tinubu

A wani rahoton kuma Fadar shugaban ƙasa ta bayyana dalilin da ya sanya shugaba Tinubu bai raba wa ministocinsa ma'aikatun da zasu riƙe ba.

Femi Gbajabiamila ya ce raba ma'aitun tun da fari zai taimaka wa majalisa wajen tantance wa, amma Tinubu ya san dukka zasu iya aiki a ko ina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262