Kaduna: Gwamna Malam Uba Sani Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 14

Kaduna: Gwamna Malam Uba Sani Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 14

  • Gwamna Uba Sani na jihar Ƙaduna ya rantsar da sabbin kwamishinoni 14 waɗanda ya naɗa a gwamnatinsa ranar Alhamis
  • Ya ce a yanzu gwamnatinsa ta ɗauki harama bayan rantsar da mutanen da zasu ja ragamar cika alƙawurran da ya ɗaukar wa al'umma
  • Uba Sani ya ce ya yi la'akari da kwarewa da cancanta wajen zaƙulo mutanen da ya naɗa a matsayin kwamishinoni

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna State - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bai wa sabbin kwamishinoni 14 rantsuwar kama aiki a Sir Kashim Ibrahim House.

Gwamna Sani ya tabbatar da haka a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023.

Uba Sani ya rantsar da kwamishinoni.
Kaduna: Gwamna Malam Uba Sani Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 14 Hoto: @Ubasanius
Asali: Twitter

Da yake jawabi kan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa da ɗauki saiti bayan rantsar da kwamishinoni 14, waɗanda zasu jagoraci kudirinsa na sauƙaƙa wa talakawa da marasa galihu.

Kara karanta wannan

Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina

A cewarsa, bikin rantsarwan ya ja hankalin ɗumbin mazauna Kaduna masu kishin ƙasa, waɗanda suka halarci wurin domin tabbatar da goyon bayansu ga gwamnatinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Mun yi la’akari da kwarewa da kuma sadaukarwa da jajircewa wajen yi wa jihar Kaduna hidima yayin zaƙulo mutanen da muka naɗa a matsayin mambobin majalisar zartarwa."

Jerin kwamishinonin da gwamnan ya rantsar da wuraren aikinsu

1. Sule Shuaibu - Antoni Janar kuma kwamishinan tsari'a

2. Shizzer Nasara Joy Bada - Kwamishinar kuɗi

3. Farfesa Muhammad Sani Bello - Kwamishinan ilimi

4. Umma Kaltume Ahmed - Kwamishinar lafiya

5. Sadiq Mamman Lagos - Kwamishinan kananan hukumomi

6. Aminu Abdullahi Shagali - Kwamishinan gidaje da raya karkara

7. Salisu Rabi - Kwamishinar harkokin al'umma da walwala

8. Farfesa Benjamin Kumai Gugong - Kwamishinan wasanni

9. Ibrahim Hamza - Kwamishinan ayyuka da kayayyakin more rayuwa

Kara karanta wannan

Cikakkun Sunaye: Gwamna Sani Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe 9 Masu Muhimmanci a Jihar Kaduna

10. Mukhtar Ahmed - Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi

11. Abubakar Buba - Kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa

12. Murtala Mohammed Dabo - Kwamishinan noma

13. Patience Fakai - Kwamishinar kasuwanci da fasahar zamani

14. Auwal Musa Shugaba - Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida.

Babbar Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar DSS Na Ci Gaba da Tsare Godwin Emefiele

A wani labarin na daban kuma Babbar Ƙotun Abuja mai zama a Maitama ta yi fatali da buƙatar hukumar DSS na ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN.

Alkalin kotun mai shari'a Hamza Muazu, ya ce buƙatar da DSS ta shigar rashin mutunta tsarin shari'a ne kuma Kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262