Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Abdullahi Adamu da Omisore a Aso Villa

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Abdullahi Adamu da Omisore a Aso Villa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin tsohon shugaban APC, Abdullahi Adamu da Sakatare, Iyiola Omisore a Villa
  • Wannan ne karo na farko da suka gana tun bayan murabus ɗin Adamu da Omisore daga matsayin shugaba da Sakataren APC
  • Har yanzun dai Adamu ko Omisore ba su fito sun bayyana cewa sun yi murabus daga muƙamansu ba

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tsohon shugaban APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakatare, Iyiola Omisore a fadarsa Aso Rock.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan gana wa na zuwa ne mako ɗaya bayan Adamu da Omisore sun yi murabus daga kan muƙamansu.

Shugaba Tinubu da Abdullahi Adamu.
Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Abdullahi Adamu da Omisore a Aso Villa Hoto: punchng
Asali: UGC

Abdullahi Adamu da Omisore sun sauka daga kujerun shugaban APC da Sakatare awanni kaɗan gabanin ranar taron shugabanni da taron majalisar zartarwa (NEC).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shetimma, Gwamnoni da Sauran Mambobin NEC Sun Sa Labule a Villa, Bayanai Sun Fito

A lokacin shugaba Tinubu yana Kenya inda ya halarci taron ƙungiyar tarayyar Afirka kuma tunda ya dawo bai zauna da tsoffin shugabannin ba sai yau Talata, 25 ga watan Yuli.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan kuma Adamu, tsohon gwamnan Nasarawa ya ƙi yarda ya ce komai kan abinda ke faruwa a APC, ya ce a jira sai Bola Tinubu ya dawo Najeriya.

Wane batu suke tattaunawa a wannan zaman a Villa?

Duk da ba bu bayani a hukumance kan abinda zasu tattauna, ana hasashen wannan gana wa zata maida hankali ne kan batutuwan da shuka shafi abinda ke wakana kan shugabancin APC.

Duk da Adamu ko Omisore ba su fito fili su bayyana murabus din nasu ba tun lokacin da aka samu labari, Mukaddashin shugaban APC, Abubakar Kyari, ya tabbatar murabus ɗin jiga-jigan 2.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Kyari, wanda ya kasance mataimakin shugaban APC (Arewa) ya shaida wa yan jarida cewa:

"Kwamitin NWC na son sanar da ku murabus din shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu, da na sakataren jam'iyya na kasa, Sanata Iyiola Omisore."

Mukaddashin shugaban APC ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan kammala taron NWC na gaggawa a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Mamban APC" Ta Fadi Sunayen Mutum 3 Da Aka Cire Daga Cikin Ministocin Tinubu

A wani rahoton na daban Ruɗanin da ke tattare da sunayen Ministocin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ake jira ya ƙara buɗe sabon shafi.

Wani kishin-ƙishin ya nuna cewa an cire sunayen wasu jiga-jigan siyasa 3 bayan da fari sunansu ya shiga cikin ministocin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262