Majalisar Dattawa Ta Dage Sanar Da Sunayen Ministocin Tinubu Zuwa Gobe Laraba

Majalisar Dattawa Ta Dage Sanar Da Sunayen Ministocin Tinubu Zuwa Gobe Laraba

  • Majalisar Dattawa ta sake dage zamanta a yau Talata kan bayyana sunayen ministocin Shugaba Tinubu
  • Wannan ba shi ne karon farko ba da majalisar ke dage zamanta wanda ke jawo cece-kuce a kasar
  • 'Yan Najeriya na dakon ganin irin mutanen da za su fito a jerin sunayen tun bayan hawan shi karagar mulki

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta dage zamanta na yau Talata zuwa gobe Laraba 26 ga watan Yuli saboda sanar da ministocinm Shugaba Bola Tinubu.

Majalisar ta dage zaman ne zuwa gobe Laraba don sanar da jerin sunayen ministoci da Shugaba Tinubu ya mika.

Majalisar Dattawa ta sake dage zamanta kan ministocin Tinubu zuwa gobe labara
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio Ya Dage Sanar Da Sunayen Ministocin Tinubu. Hoto: Nigerian Senate.
Asali: Facebook

PM News ta tattaro cewa Tinubu ya mika sunayen ministocin tun a makon da ya gabata ga magatakardar majalisar.

Majalisar ta dage zaman majalisar ba tare da wani dalili ba

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Zai Sanar Da Jerin Ministocinsa a Yau, Cikakken Bayani Ya Bayyana

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele shi ya bayyana daga zaman a yau Talata 25 ga watan Yuli ba tare da fadin dalili ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Simon Mwadkwon ya goyi bayan dage zaman zuwa gobe Laraba 26 ga watan Yuli, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

'Yan Najeriya na dakon sunayen ministocin tun bayan hawan Shugaba Bola Tinubu karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Mutane na ganin sunayen ministocin zai ba wa mutane mamaki

Masana na hasashen cewa sunayen ministocin za su zo da abin mamaki ganin yadda shugaban ke ba ta lokaci akai kusan watanni biyu kenan da hawan shi mulki.

Wasu na zargin bata lokacin bai rasa nasaba da sauye-sauye da ake samu a cikin jerin sunayen da kuma siyasa da ta shiga cikin lamarin.

Kara karanta wannan

Za a Fito da Sunayen Ministoci, Gwamnoni da Tsofaffin Gwamnonin APC Sun Huro Wuta

Yayin ake sa ran 'yan adawa da dama ka iya ganin sunayensu a cikin jerin sunayen da suka hada da tsoffin gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki.

Jerin Mataimakan Shugabannin Majalisar Dattawa 4 Da Aka Yi A Najeriya

A wani labarin, shugaban majalisar Dattawa shi ne na uku a girma a Najeriya bayan shugaban kasa da mataimakinsa.

Mai bi masa shi ne mataimakin shugaban majalisar, wato Barau Jibrin wanda aka zaba kwanan nan a majalisar.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin mataimakan shugaban majalisar da aka taba yi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.