Gwamna Uba Sani Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Kaduna

  • Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna ya yi sabbin naɗe-naɗe masu muhimmanci a gwamnatinsa
  • Sabbbin mutanen da gwamnan ya naɗa na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai, Muhammad Lawal Shehu ya fitar
  • Ya ce naɗe-naɗen zasu fara aiki nan take kuma mai girma gwamna ya taya mutanen murna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna State - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ƙara yin wasu sabbin naɗe-naɗe masu matuƙar muhimmanci a gwamnatinsa.

Gwamnan ya naɗa shugabannin hukumomi, manyan masu ba shi shawara ta musamman da hadimai.

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Gwamna Uba Sani Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Kaduna Hoto: @Govkaduna
Asali: Twitter

Wannan na kunshe a wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Tuwita mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labaransa, Muhammad Lawal Shehu.

Uba Sani ya bayyana cewa ya yi la'akari da tarihin siyasa, gaskiya da riƙon amana da sadaukarwa wajen gina jihar Kaduna yayin zaƙulo mutanen da ya naɗa muƙaman.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Sake Nada Dukkanin Kwamishinonin Magabacinsa, Ya Bayyana Dalilansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma ya taya su murna kana ya buƙaci su yi amfani da dabaru da tsare-tsaren masu kyau wajen tafiyar da harkokin wuraren da aka ba su amana.

Jerin mutanen da Uba Sani ya naɗa

Sanarwan ta ce a wani yunkuri na kara habaka harkokin mulki a Kaduna da kuma cika alkawuran yakin neman zabe, mai girma gwamna Uba Sani, ya amince da nade-naden mukamai kamar haka:

1. Mohammad Sada Jalal - Darakta Janar na hukumar kula da harkokin filaye ta Kaduna (KADGIS).

2. Jerry Adams - Muƙaddashin shugaban hukumar tattara harajin cikin gida (KADIRS).

3. Adamu Magaji - Shugaban hukumar kula da kayayyakin gwamnatin Kaduna (KADFAMA).

4. Adamu Sama'ila - Mashawarci na musamman kan harkokin kwadugo

5. Amina Sani Bello - Babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin ɗalibai

6. Salisu Ibrahim Garba - Babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bankaɗo Badaƙalar Maƙudan Kuɗi, Ya Ceto Biliyan N1.2 Daga Ma'aikata

7. Larai Sylvia Ishaku - Babbar mataimakiya ta musamman kan tsare-tsaren walwala

8. Clement Shekogaza Wasah - Babban mataimaki na musamman kan harkokin al'umma

9. Waziri Garba - Babban mataimaki na musamman kan harkokin gudanarwa.

"Dukkan waɗan nan naɗe-naɗe zasu fara aiki ne nan take," inji Sakataren watsa labaran gwamna, Muhammad Lawal Shehu.

Mutanen El-Rufai Sun Dawo Cikin Sababbin Kwamishonin Gwamna Uba Sani a Kaduna

A wani rahoton Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya aikawa majalisar dokoki sunayen wadanda yake so a nada a matsayin sababbin Kwamishononi.

Sunayen wadanda aka za a nada sun hada da Farfesa Muhammad Sani Bello wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman takarar Uba Sani a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262