Da Duminsa: Shugaban Kasa Tinubu Zai Sanar Da Jerin Ministocinsa a Yau, Cikakken Bayani Ya Bayyana
- Ga dukkan alamu jerin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ake ta zuba idon gani za su bayyana a wannan karshen mako na Yulin 2023
- Wani hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce jerin sunayen ministocin, da bayanan wadanda za su kafa majalisar Tinubu zai bayyana a yau, Talata, 25 ga watan Yuli
- A cewar Bashir Ahmad, za a sanar da sunayen ministocin a zaman majalisa domin hana wasu sauye-sauye na kurarren lokaci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi karin jawabi game da jerin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ake ta zuba idon gani.
A cewar Bashir Ahmad, Tinubu zai bayyana jerin ministocinsa a ranar Talata, 25 ga watan Yuli.
Majalisar dattawa za ta karbi jerin ministocin Tinubu a ranar Talata, 25 ga watan Yuli, hadimin Buhari ya bayyana
Ahmad, tsohon hadimin Buhari a kafofin sadarwar zamani ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, a daren ranar Litinin, 24 ga watan Yuli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya bayyana cewa za a sanar da jerin sunayen a zauren majalisar dattawa a ranar Talata, 25 ga watan Yuli, matukar babu wani sauye-sauye na kurarren lokaci.
Ya rubuta a shafin nasa:
"Domin hana sauye-sauye na kurarren lokaci.
"Za a sanar da jerin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ake ta zuba idon ganinsu a majalisar dattawa a gobe Talata."
Legit.ng ta fahimci cewa shugaban kasar na da sauran kwanaki biyar ya cika kwanaki 60 na gabatar da jerin ministocinsa domin majalisa ta tantance ta tabbatar da su, kamar yadda yake a kungin tsarin mulkin 1990 da aka yi wa kwaskwarima.
Gwamna Bala Muhammad ya tura sunayen kwamishinoni 24 majalisar dokokin Bauchi
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya aike wa majasar dokokin jihar da sunayen mutanen da yake son nada wa kwamishinoni.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya tura sunayen mutane 24 ga majalisar dokokin Bauchi domin tantance su da kuma tabbatar da su a matsayin kwamishinoni.
Kakakin majalisar, Abubakar Y. Suleiman, ne ya karanta sakon mai girma gwamna a zaman majalisar na ranar Litinin, 24 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng