Shugaba Tinubu Ya Cire Sunayen Wike da Ganduje Daga Cikin Ministoci? Gaskiya Ta Fito
- Babban jigon APC ya yi kira ga magoya bayan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da na Nyesom Wike su kwantar da hankulansu
- Ya ce raɗe-raɗin da ke yawo cewa shugaba Tinubu ya cire sunayen tsoffin gwamnonin daga jerin ministoci ba gaskiya bane
- A wata hira, kodinetan ƙungiyar yaƙin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci mutane su yi fatali da jita-jitar baki ɗaya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - An roƙi makusanta da magoya bayan tsoffin gwamnonin Kano da Ribas, Abdullahi Ganduje da Nyesom Wike su kwantar da hankulansu kan raɗe-raɗin da ke yawo.
Wani rahoton Daily Independent ya nuna cewa da yiwuwar shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zare sunan Ganduje da Wike daga cikin jerin ministocin da zai naɗa.
An ce shugaban ƙasar ya ɗauki wannan matakin kan tsoffin gwamnonin ne bayan nazari kan rahoton binciken hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Sauƙi Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Zata Karya Farashin Abinci a Jihohi, Ta Bada Sabon Umarni Ga NEMA da CBN
Wike ya fara ɗaga wa Tinubu murya bayan cire sunansa
Wasu rahotanni sun yi ikirarin Nyesom Wike ya fara sukar Tinubu bayan jin labarin an cire sunansa da na tsohon gwamnan Kano, Ganduje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma shugaban ƙungiyar magoya bayan Bola Ahmed Tinubu (BAT-V), Chief Tony Okocha, ya yi watsi da rahoton cewa an cire sunan Wike da Ganduje.
Ya ce ba bu tantama wannan jita-jitar da ake yaɗa wa wani tuggun masu hana ruwa gudu ne amma ba bu ƙanshin gaskiya.
Jigon jam'iyyar APCn ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Ribas na jam'iyyar PDP mutum ne mai hazaƙa da ya cimma nasarori masu dumbin yawa, wanda 'yan Najeriya ƙe ƙaunarsa.
Menene gaskiyar raɗe-raɗin cire sunan Ganduje da Wike?
A cewar Mista Okocha, Wike yana kaunar shugaban ƙasa Tinubu shiyasa ya mara masa baya a zaben 2023 a jihar Ribas, inda ya ƙara da cewa jita-jitar ƙarya ce ba ta da tushe.
Okocha ya ƙara da cewa wanda ke yaɗa labarin ba ma'aikacin hukumar DSS bane kuma ba shi da alaƙa da fadar shugaban ƙasa.
Daga nan sai ya jefa tambaya da cewa:
"A ina ya samu labarin hukumar tsaron farin kaya ta cire sunan Nyesom Wike?"
Tsohon Sanatan PDP Ya Yi Babban Rashi, Matarsa Ta Rasu a Abuja
A wani labarin kuma Ɗan majalisa mai wakiltar jihar Abiya ta arewa a majalisar dattawa ta 8 ya yi rashin matarsa, Lady Nimi Ohuabunwa.
Marigayya matar sanatan, wacce ta sha fama da jinyar wata cuta tsawon lokaci, ta mutu ne ranar Asabar, 22 ga watan Yuli a Asibitin Abuja.
Asali: Legit.ng