Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince da Karin Kwamishinoni Biyu
- Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin karin kwamishinoni 2 da Abba Kabir Yusuf ya aiko mata
- A zaman majalisa na ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, 2023, ta tantance Sheikh Tijani Auwal da kuma Hajiya Aisha Lawal-Saji
- Zuwa yanzun, majalisar dokokin ta amince da naɗin kwamishinoni 22 a gwamnatin Abba Gida-Gida
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano state - Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance da kuma amince wa da naɗin ƙarin kwamishinoni biyu waɗanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aiko mata.
Rahoton The Nation ya ce hakan ya biyo bayan nasarar tsallake matakin tantancewa da kwamishinonin biyu suka yi a zaman majalisa na ranar Litinin, 24 ga watan Yuli.
Shugaban majalisar dokokin Kano, Honorabul Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman tantance kwamishinonin biyu a birnin Kano.
Karin kwamishinonin da majalisar ta amince da naɗin su sun haɗa da babban Malamin Islama, Sheikh Tijani Auwal da kuma mace, Hajiya Aisha Lawal-Saji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abinda kakakin majalisa ya faɗa wa kwamishinonin 2
Da yake jawabi, shugaban majalisar ya buƙaci sabbin kwamishinonin su bai wa maraɗa kunya ta hanyar aiki tuƙuru a duk ma'aikatun da mai girma gwamna ya tura su.
Ya kuma roƙi su haɗa kai da gwamna Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida wajen samar da dumbin ci gaba a jihar Kano, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Mutanen biyu sun nuna farin ciki da shiga gwamnatin Abba
Da suke jawabi ga yan jarida jim kaɗan bayan tantance su, sabbin kwamishinonin sun bayyana farin cikinsu bisa naɗin da gwamna Abba Gida Gida ya musu.
Sun ayyana wannan naɗi da kiraan yi wa kanawa aiki kuma sun yi alkawarin cewa za su bada gudummuwa bakin gwargwado wajen kawo ci gaba a Kano.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa zuwa yanzu majalisar Kano ta tantance tare da amince wa da naɗin kwamishinoni 22.
Kotu Ta Tabbatar Da Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Sanatan Kano Ta Tsakiya
A wani rahoton kuma Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe mai zamanta a birnin Kano ta yanke hukunci akan ƙarar AA Zaura da Sanata Rufa'i Hanga.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da AA Zaura ya shigar inda ta tabbatar da Hanga a matsayin zaɓaɓɓen sanatan Kano ta tsakiya.
Asali: Legit.ng