Kotu Ta Rushe Nasarar Dan Majalisar Wakilan Jam’iyyar Labour a Delta, Ta Mayarwa Elumelu Na PDP Kujerar

Kotu Ta Rushe Nasarar Dan Majalisar Wakilan Jam’iyyar Labour a Delta, Ta Mayarwa Elumelu Na PDP Kujerar

  • Kotun sauraron kararrakin zabe da ke jihar Delta ta rushe nasarar Ngozi Okolie na jam'iyyar Labour
  • Kotun ta ayyana Honarabul Ndudi Elumelu a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gabata na watan Fabrairun 2023
  • Kotun ta kafa hujja da cewa Okolie ba cika sharadin zama halastaccen dan jam'iyyar ta Labour ba a lokacin da aka gudanar da zabe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Asaba - Kotun sauraron kararrakin zabe da ke Asaba babban birnin jihar Delta, ta soke nasarar Ngozi Okolie na jam'iyyar Labour a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Aniocha/Oshimili.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ayyana Okolie matsayin wanda ya lashe zaben na watan Fabrairun 2023 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kotu ta karbe nasarar dan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Labour a Delta
Kotun kararrakin zabe ta kwace kujerar dan Majalisar Wakilai na jam'iyyar Labour, ta bai wa na jam'iyyar PDP nasara a Delta. Hoto: Yinka Hafiz
Asali: Facebook

Kotu ta bai wa Tony Ndudi nasara saboda shi ne ya zo na biyu a zaben

Kara karanta wannan

Ganduje vs Al-Makura: Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Ya Kamata APC Ta Nada a Matsayin Shugabanta Na Kasa

Sai dai kotun zaben a yayin da take yanke hukunci a ranar Litinin, ta ayya Honarabul Ndudi Elumelu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun ta ayyana Elumelu a matsayin wanda ya lashe zaben kasancewarsa wanda ya zo na biyu a zaben da ya gabata.

A lokacin da aka gudanar da zaben, Okolie na LP ya samu kuri'u 53,879, Ndudi Elumelu na PDP ya samu 33,456, yayin da Tony Nwaka na APC ya samu kuri'u 11,712.

Dalilin da ya sa kotun ta soke zaben Okolie na jam'iyyar Labour

Kotun sauraron kararrakin zaben a yayin da take yanke hukunci, ta bayyana cewa Okolie ba dan jam'iyyar Labour ba ne har bayan ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2022.

A dokar kasa, duk wanda bai shiga jam'iyya kafin 28 ga watan Mayun ba, wanda a lokacin ne ake gabatar da zaben cikin jam'iyyu, ba zai iya fitowa takara a cikinta a kakar zabe ba.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kano: Abba Gida Gida Ya Rufe Shari’a Da Baffa Bichi a Matsayin Shaida Shi Kadai

A bisa wannan hujjar ce kotun kararrakin zaben ta soke nasarar da Ngozi Okolie ya samu, tare da hannantata ga mai biye masa, Honarabul Ndudi Elumelu.

Ndudi Elumelu shi ne tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ta tara da ta shude kamar yadda PM News ta wallafa.

Atiku ya ce babu abinda zai faru idan kotu ta tsige Tinubu daga kujerarsa

Legit.ng a baya ta kawo muku martanin da dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi dangane da shari'ar da yake da Tinubu.

Atiku ya ce sama ba za ta fado ba idan kotun ta tsige Tinubu daga kan matsayinsa na shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng