Abdullahi Ganduje Ya Huro Wuta Wajen Ganin Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC
- Da alama Abdullahi Umar Ganduje ba da wasa yake yi wajen zama sabon shugaban APC a Najeriya
- Tsohon Gwamnan Kano ya ziyarci wasu jagororin APC da kusoshin Gwamnati domin cin ma burinsa
- Shugabannin APC a Arewa maso tsakiya su na ganin yankinsu aka warewa shugabancin jam’iyya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Abdullahi Umar Ganduje ya dage wajen ganin ya karbi kujerar shugaban jam’iyyar APC, a sakamakon murabus da Abdullahi Adamu ya yi.
Punch ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya fito daga Arewa maso yamma, yana kokarin ganin jagororin jam’iyyar APC sun goyi bayan shi.
Inda burin tsohon Gwamnan zai gamu da cikas shi ne jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa maso tsakiya su na ganin su aka warewa kujerar.
PGF ta na tare da Ganduje?
Zuwa yanzu ana tunanin Abdullahi Ganduje ya samu goyon bayan Mai girma shugaban kasa da kuma kungiyar Gwamnonin jihohin APC na PGF.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
‘Yan kungiyar ta PGF sun yi zama a garin Abuja, ana tunanin a nan Gwamnonin su ka yarda cewa za su goyi bayan Ganduje ya gaji Abdullahi Adamu.
Ganduje ya yi zama da Akume, Wammako
Wata majiya ta ce ‘dan siyasar ya zauna da Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume duk saboda yunkurin ganin ya karbi ragamar NWC.
Wata majiya ta shaidawa jaridar a boye cewa Ganduje ya hadu da Akume wanda yana cikin kusoshin APC a Arewa, saboda ya mara masa baya a APC.
Kafin nan kuma fitaccen ‘dan siyasar ya ziyarci tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a gidansa a Asokoro a Abuja.
Cikas daga Arewa maso tsakiya
Ba mu da labarin matsayar Gwamnonin APC na jihohin Nasarawa, Kogi, Kwara, Neja, da kuma Benuwai da su ka fito daga yankin Arewa maso tsakiya.
Jam’iyyar PDP mai adawa ce ta ke rike da Filato, APC ta na da iko da sauran jihohin bangaren.
Shugaban APC na jihar Nasarawa, John Mamman ya shaidawa ‘yan jarida tun a bara, yankinsu na Arewa maso tsakiya aka warewa shugabancin jam’iyyar.
Da yake magana a garin Lafiya, Mamman ya ce idan da adalci, kujerar ta na hannunsu.
Shirin nadin sababbin Ministoci
Abdullahi Umar Ganduje ya canza lissafi jim kadan bayan Shugaban Jam'iyyar APC ya sauka daga mukaminsa, da farko an ji labari an yi tunanin ba shi Minista.
Har yanzu sunayen wadanda za su iya zama Ministocin tarayya bai bar Aso Rock ba, ana ta ‘yan canje-canje, sai dai kwanaki kadan su ka ragewa Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng