Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ya Sake Nada Kwamishohin Magabacinsa, Ya Bayyana Dalilansa

Gwamnan Jihar Akwa Ibom Ya Sake Nada Kwamishohin Magabacinsa, Ya Bayyana Dalilansa

  • Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sake naɗa kwamishinonin da suka yi aiki a gwamnatin magabacinsa, Udom Emmanuel
  • Eno ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin ya sakawa waɗanda suka goya masa baya lokacin fafatawar neman cin zaɓe
  • Gwamnan na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa ya yi amanna cewa haƙƙin zaɓar mutanen da zai yi aiki da su ya rataya ne a wuyansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Uyo, jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sake naɗa dukkanin kwamishinonin da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin magabacinsa, Udom Emmanuel.

Business Day ta rahoto cewa dukkanin kwamishinoni da wani mai bayar da shawara na musamman da suka yi aiki a ƙarƙashin tsohon gwamna Emmanuel, an sake naɗa su a cikin waɗanda za su yi aiki a gwamnatin gwamna Eno.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bankaɗo Badaƙalar Maƙudan Kuɗi, Ya Ceto Biliyan N1.2 Daga Ma'aikata

Gwamna Uno ya sake nada kwamishinonin magabacinsa
Gwamna Uno ya sake nada kwamishinonin da suka yi aiki a gwamnatin tsohon gwamna Udom Hoto: UDOM Emmanuel, Pastor Umo Eno
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da aka aike zuwa ga majalisar dokokin jihar.

Tsohon gwamna Udom dai ya zaɓi Eno a matsayin magajinsa a lokacin babban zaɓen shekarar 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin da ya sanya na sake naɗa kwamishinonin tsohon gwamna Emmanuel, Eno ya bayyana

Da yake jawabi kan dalilin da ya sanya ya yi hakan, gwamna Eno ya yi bayanin cewa hakan da ya yi wata hanya ce ta wucin gadi domin sakawa waɗanda suka yi gumurzu tare da shi wajen cin zaɓe, a lokacin da ƴan adawa suka yi ƙarfi a jihar.

Leadership ta ambato gwamnan na cewa:

"Waɗannnan mutanen sun je yaƙi tare da ni, mun leƙa lungu da saƙo tare da su kuma mun yi nasara. Ta ya zan saka musu, watsi zan yi da su?"

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

"Sun ɗauki ragamar aikin sun bani. Su taimaka su kyaleni na zaɓi waɗanda na yi amanna za su gudanar da aikin. Ba zai yiwu ku bani aiki ba sannan ku ce za ku zaɓar min waɗanda za su yi aikin tare da ni."
"Na yi amanna cewa alhakin zaɓar mutanen da za su yi aiki tare da ni ya rataya ne a wuyana. Al'ummar Akwa Ibom da aikin da na yi yakamata su yanke min hukunci."

Manyan Jiga-Jigan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC

A wani labarin kuma, jam'iyyar PDP ta samu koma baya a jihar Ondo bayan wasu manyan jiga-jiganta sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP su 63 ne dai suka tsallaka zuwa jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Idanre ta jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng