Zaben Gwamna: Abba Yusuf Ya Rufe Shari’a Da SSG a Matsayin Shaida Shi Kadai

Zaben Gwamna: Abba Yusuf Ya Rufe Shari’a Da SSG a Matsayin Shaida Shi Kadai

  • An ci gaba da zaman sauraron shari'a a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli
  • Abba Gida Gida ya rufe shari'arsa da sakataren gwamnatin jihar, Dr Abdullahi Baffa Bichi a matsayin shaida shi kadai
  • Jam'iyyar APC na karar hukumar INEC kan ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano na ranar 18 ga watan Maris din 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rufe shar'iarsa a matsayin wanda ake kara na biyu a shari'ar da ke guda a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano da sakataren gwamnatin jihar, Dr Abdullahi Baffa Bichi a matsayin shaida shi kadai.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mai karar, APC, tana kalubalantar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) kan ayyana Abba na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris 2023.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Tsohuwar Kwamishiniya Ta Rasu a Jihar Kano

Abba Kabir ya rufe shari'arsa a kotun zaben Kano da shaida1
Zaben Gwamna: Abba Yusuf Ya Rufe Shari’a Da SSG a Matsayin Shaida Shi Kadai Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

An ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya doke Gawuna da tazarar kuri'u 128,897

Mai karar ta kuma bukaci kotun zabe da ta ayyana cewa NNPP bata da dan takara domin Abba baya cikin rijistansu na masu zabe da aka gabatarwa INEC a lokacin zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda ake karar sun hada da INEC, Abba Kabir Yusuf da kuma jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

A zaman sauraron shari'ar da aka ci gaba da yi a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, lauyan wanda ake kara na biyu, R. A. Lawal SAN, ya jagoranci shaidun da ya gabatawajen daukar rantsuwa a gaban kotu a matsayin shaidarsa.

Baffa Bichi ya fada ma kotun cewa an ayyana wanda ake kara na biyu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 20 ga watan Maris bayan ya samu kuri'u 1,019,602 wajen doke Dr Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) wanda ya samu kuri'u 890,705 da tazarar kuri'u 128,897, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

To fah: Atiku ya tada hankalin Tinubu, ya fadi hujja 1 a kotu, ya ce kawai a tsige Tinubu a ba shi Najeriya

Jiga-jigan PDP 63 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Ondo

A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta hadu da gagarumin tangarda a sansaninta.

Hakan ya kasance ne yayin da jiga-jigan PDP 63 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a karamar hukumar Idanre ta jihar Ondo a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng