Shugaba Ya Rubutawa Gwamnoni Wasika Game da Shirin ba Ganduje Shugabancin APC
- Salihu Lukman ya aika wasika zuwa ga Gwamnonin APC a kan abubuwan da ke faruwa a Jam’iyya
- Mataimakin shugaban na APC a matakin kasa ya zargi ‘yan kungiyar PGF da yin adalci a jam’iyya
- A matsayin shugaban Arewa maso yamma, Lukman yana ganin Gwamnoninsu sun sabawa tsari
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban APC na Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya rubuta takarda zuwa ga gwamnonin da ke mulki a jam’iyya mai-mulki.
Vanguard ta ce Alhaji Salihu Lukman ya aika wasika zuwa ga Gwamnan jihar Imo, yana gargadi kan yin adalci game da wanda zai zama shugaban APC.
Gwamnan Imo, Hope Uzodinma shi ne shugaban kungiyar PGF ta gwamnonin jihohin APC.
Lukman ya rubuta wasikar ne a ranar 21 ga watan Yuli, yana cewa ya kamata gwamnoni su zama tamkar kwakwalwar APC a halin da aka shiga.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba a yi adalci ba" In Ji Lukman
"Abin takaici ne ana rahoto kungiyar Gwamnoni na PGF a karkashin jagorancinka sun yanke shawarar yarda Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaban APC.
Duk da cewa ku na da hakki a matsayin muhimman jigo a APC, ku goyi bayan wani ‘dan takara a wajen zama shugaban jam’iyya na kasa har ku iya fitowa fili ku bayyana haka...
...wannan rashin adalci ne ga shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin da ba su cikin kungiyar PGF da shi kan shi Abdullahi Umar Ganduje da aka tsaida."
- Salihu Lukman
Lukman ba bako ba ne a PGF
Jaridar ta ce a wasikar, Lukman ya fadawa Uzodinma yadda ya rike kujerar Darekta Janar a kungiyarsa ta PGF, ya ce ya san yadda abubuwa suke.
Kafin gwamnonin su cin ma matsaya, mataimakin shugaban na APC ya ce ya kamata a fara zama da NWC a game da wanda zai jagorance su.
A bisa al’ada, tsohon Darekta Janar din ya ce kyau gwamnonin jihohin su shawo kan shugabanni da sauran jagororin jam’iyya, ba a ji kurum a labarai ba.
A karshe, wasikar tayi kira ga shugaban PGF ya yi abin da aka saba, a bar jam’iyya ta dauki matakin da ya dace ta yadda za ayi wa kowa adalci a APC.
Dalilin yin waje da Abdullahi Adamu
A wani rahoto, kun ji wasu abubuwan da suka jawo shugaban APC ya yi murabus, daga ciki Abdullahi Adamu ya manta da aikin kwamitin yin sulhu.
A maimakon zama adali, shugaban ya fito karara yana goyon bayan wani ‘dan takara a zaben tsaida gwani, kuma ya cigaba da takalo shugaban kasar.
Asali: Legit.ng