Rikicin APC: Tsohon Gwamnan Jihar Osun Zai Maye Gurbin Omisore? Gaskiya Ta Bayyana

Rikicin APC: Tsohon Gwamnan Jihar Osun Zai Maye Gurbin Omisore? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wani sabon lamari ya fito a ƙoƙarin da jam'iyyar All Progressive Congress (APC) take na ƙoƙarin ganin dawo da daidaito a shugabancinta
  • Majiyoyi a fadar shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa an samu ɗan takarar da zai maye gurbin Sanata Iyiola Omisore a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa
  • Akwai yiwuwar tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya zama wannan ɗan takarar bayan ya cimma yarjejeniya da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An fara yaɗa jita-jita kan cewa wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progress Congress (APC), na shirin zama waɗanda za su maye gurbin Sanata Iyiola Omisore a matsayin sakaraten jam'iyyar na ƙasa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola da tsohon kakakin majalisar dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ana musu ganin waɗanda za su maye gurbin Sanata Omisore.

Kara karanta wannan

Babban Jigon Adawa Kuma Ɗan Takara a 2023 Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa, Ya Faɗi Dalilai

Oyetola zai zama sakataren jam'iyyar APC na kasa
Majiyoyi sun bayyana cewa an kammala shirin ba Oyetola kujerar sakataren jam'iyyar Hoto: Senator Iyiola Omisore
Asali: Facebook

Oyetola ya ziyarci Villa

An tattaro cewa, an hango Oyetola a fadar shugaban ƙasa ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli, duk da cewa Shugaba Tinubu baya nan, inda ya halarci bikin yaye sojoji a makarantar sojoji dake Jaji jihar Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni sun nuna cewa mataimakin Shugaban ƙasa, Kashin Shettima, ya yi wa Oyetola kyakkyawar tarba bayan ya isa Villa.

Wani majiya a fadar shugaban ƙasar ya bayyana cewa Oyetola ya sanya labule da Shettima a lokacin ziyarar, inda suka tattauna akan yiwuwar zamansa sakataren jam'iyyar APC na ƙasa.

Majiyar ya bayyana cewa da farko Oyetola ya nuna baya son karɓar tayin saboda aniyarsa ta yi takara a zaɓen gwamnan jihar Osun na shekarar 2026. Sai dai, daga baya ya yarda da tayin da aka yi masa.

'Yan NWC Na Adawa Da Zaman Ganduje Shugaban APC

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Tona Asirin Babban Dalili 1 Da Ya Jawo Shugaban APC da Sakatare Suka Yi Murabus

A wani labarin kuma, neman zama shugaban jam'iyyar APC da tsohon gwamnan jihar Kano, Abudullahi Umar Ganduje, yake yi na samun tangarda daga wajen ƴan kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar.

Ƴan kwamitin na nuna adawarsu da zaman Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC, saboda tsohon gwamnan ya fito ne daga yankin Arewa maso Yamma, bayan yankin Arewa ta Tsakiya ke riƙe da kujerar shugabancin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng