Daga Karshe, Majalisar Dattawa Ta Yi Magana Kan Ministocin da Tinubu Zai Naɗa
- Jinkirin shugaba Bola Tinubu wajen miƙa sunayen Ministoci ka iya tilasta wa majalisar dattawa ɗaga hutunta na shekara-shekara
- A ranar 27 ga watan Yuli majalisar zata tafi hutu amma wata majiya daga majalisar dattawa ta ce ana sa ran isowar sunayen ministoci a farkon mako mai zuwa
- Mai magana da yawun majalisar dattawa ya ce har yanzun ba a bayyana ranar da Sanatoci zasu tafi hutu ba, don haka ba dalilin musu kan batun
FCT Abuja - Da yiwuwar majalisar dattawa ta ɗage shirinta na tafiya hutun shekara yayin da ake tsammanin isowar sunayen ministocin shugaban ƙasa domin tantance wa.
A rahoton da jaridar The Nation ta tattara, Sanatoci na tsammanin shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aiko da sunayen ministocin a farkon mako mai zuwa.
Meyasa Sanatoci zasu fasa tafiya hutu?
Ɗaya daga cikin shugabannin majalisar dattawa ya ce ana tsammanin Sanatoci zasu tafi hutunsu na shekara daga ranar 27 ga watan Yuli, 2023 zuwa watan Satumba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai a cewarsa, mambobin majalisar dattawan a shirye suke su riƙa zama kowace rana domin tabbatar da sun tantance Ministocin da aka naɗa, koda hakan zai jawo ɗaga tafiya hutun da mako ɗaya.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce majalisar na da isasshen lokacin duba buƙatar shugaban kasa kafin tafiya hutu.
A cewarsa, har yanzu ba a sanar da ranar tafiya hutun shekara ba a majalisar dattawa, saboda haka tambaya kan yiwuwar ɗaga lokacin bata taso ba kwata-kwata.
Majalisar dattawa za ta yi nazari kan Ministocin Tinubu
A kalamansa ya ce:
"Akwai isasshen lokacin gabatar da sunayen ministocin da kuma tantance su."
Adaramodu ya jaddada cewa majalisar tarayya zata yi abinda ya dace kuma ba zata yi kuskuren bai wa yan Najeriya kunya ba.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ƙasa Tinubu ya tura sunayen ministocin ga hukumar yan sandan farin kaya (DSS) da hukumar yaƙi da rashawa (EFCC) domin tantance su.
"N8,000 Kudi Ne Masu Yawa" Gwaman Sule Ya Kare Tallafin Shugaba Tinubu
Kuna da labarin Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce N8,000 kuɗi masu yawa a wurin wasu iyalai da dama a Najeriya masu fama da talauci.
Gwamnan ya tunatar da cewa iyalai da yawa ne suka ci gajiyar N5,000 da aka raba a baya a matsayin tallafi, yana mai cewa matakin na yanzu ya yi daidai.
Asali: Legit.ng