Bidiyon Dala: Ta Kwabewa Ganduje, Yayin Da Gwamnatin Kano Ta Dauko Babban Lauya Femi Falana
- Hukumar yaki da cin hanci da karɓar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC), ta ce ta ɗauko hayar babban lauya Femi Falana
- PCACC ta bayyana cewa Falana zai taimaka mata kan shari'ar da take yi da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje
- Hukumar ta ce Falana zai jagoranci lauyoyi shida a madadinta a shari'ar da za su sake yi da Ganduje a ranar 25 ga watan Yuli
Kano - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Karɓar Korafe-korafe ta Jihar Kano (PCACC), ta sanar da cewa ta kirawo babban lauyan nan ɗan rajin kare haƙƙin bil'ama, Femi Falana (SAN).
Falana zai taimakawa hukumar ne a shari'ar da take yi da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, inda ya nemi kotu ta dakatar da binciken da hukumar ke yi kan bidiyonsa na karbar cin hancin dala.
Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana
Lauyan hukumar Usman Fari ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan ɗage sauraron ƙarar da kotu ta yi zuwa ranar 25 ga watan Yuli kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Dage shari’ar ya biyo bayan lauyan Ganduje, Basil Hemba, da ya shaidawa kotun cewa wanda yake karewa na buƙatar ƙarin lokaci domin amsa ƙarar da hukumar ta shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Femi Falana zai jagoranci lauyoyi shida a madadin hukumar
Usman ya bayyana cewa a zaman da za a yi na ranar 25 ga watan Yuli, Femi Falana ne zai jagoranci lauyoyi shida a madadin hukumar ta PCACC.
A kalamansa:
“Hukumar ce ta ɗauko shi domin ya jagorance mu kan lamarin kuma a shirye muke mu ci gaba da shari’ar.”
An ta tattaro cewa, da safiyar Juma’a ne aka tsara cewa babban lauyan zai iso Kano domin ya jagoranci tawagar amma hakan ba ta samu ba, sakamakon samun matsalar a jirgin da zai hawo.
Kotu ta hana hukumar ta PCACC gayyata ko tuhumar Ganduje
Idan za a iya tunawa, Ganduje ya nemi babbar kotun tarayya da ke Kano da ta tabbatar masa da 'yancinsa da yake da shi na ɗan ƙasa wanda ya haɗa da mallakar kadarori da kuma gabatar da rayuwarsa yadda doka ta ba shi dama.
Hakan ya biyo bayan gayyatar da hukumar ta PCACC ta yi masa domin ya amsa wasu tambayoyi dangane da bidiyon da aka gan shi yana cusa dalolin da ake zargi na cin hanci ne a aljihunsa.
Dangane da haka ne kotun wacce mai shari'a A.M. Liman ke jagoranta ta dakatar da hukumar ta PCACC da sauran hukumomi bakwai daga gayyata ko kama tsohon gwamnan kan bidiyon na dala kamar yadda Thisday ta ruwaito.
Abba Gida Gida ya dakatar da shugabannin makarantun sakandire 3 saboda sakaci
Legit.ng a baya ta kawluku wani rahoto kan dakatarwar da gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi wa wasu shugabannin makarantun sakandire na jihar.
Hakan ya biyo bayan zarginsu da gwamnatin ta yi da sakaci da wuraren aikinsu bayan ziyarar bazata da gwamnan ya kai a makarantunsu.
Asali: Legit.ng