Gwamnoni 11 Sun Ziyarci Tsohon Shugaban APC Ta Kasa, Abdullahi Adamu

Gwamnoni 11 Sun Ziyarci Tsohon Shugaban APC Ta Kasa, Abdullahi Adamu

  • Gwamnoni 11 na jam'iyyar APC sun ziyarci tsohon shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu a gidansa da ke birnin tarayya Abuja
  • Tawagar gwamnoin sun roƙi tsohon gwamnan da ya ci gaba da mara wa jam'iyyar APC baya duk da ya yi murbus
  • Sanata Adamu ya tabbatar da cewa ya karɓi bakuncin gwamnonin, a cewarsa sun je yaba masa ne bisa jagorantar APC zuwa ga nasara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 11 sun ziyarci tsohon gwamnan Nasarawa kuma tsohon shugaban jam'iyya na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Adamu ya yi murabus daga matsayin shugaban jam'iyyar APC ranar Lahadi da ta gabata.

Gwamnonin jam'iyyar APC da Sanata Adamu.
Gwamnoni 11 Sun Ziyarci Tsohon Shugaban APC Ta Kasa, Abdullahi Adamu Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Gwamnonin, karƙashin ƙungiyar gwamnonin APC (PGF) sun kai wa Adamu ziyara ne bisa jagorancin shugabansu kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Tona Asirin Babban Dalili 1 Da Ya Jawo Shugaban APC da Sakatare Suka Yi Murabus

Tawagar gwamonin ta kai wa Adamu ziyara har gidansa da ke cikin birnin tarayya Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin gwamnonin da suka gana da Adamu

Gwamnonin jam'iyya mai mulki da aka hanga a gidan Sanata Adamu sun haɗa da na jihohin Katsina, Ebonyi, Sakkwato, Neja, Gombe, Benuwai, Jigawa, Imo, Ogun, Kebbi da kuma muƙaddashin gwamnan jihar Ondo.

Tawagar gwamnonin, waɗanda suka roƙi tsohon gwamnan da ya ci gaba da mara wa APC baya, sun shafe kusan awa guda a gidansa suna gana wa.

Menene dalilin wannan ziyara?

Wata majiya daga gidan Sanata Adamu ta shaida wa jaridar cewa gwamnonin sun kuma yaba wa tsohon shugaban jam'iyyar bisa matakin da ya ɗauka na murabus domin kishin APC.

Majiyar ta ce:

"Sun gode masa bisa jagorantar jam'iyyar zuwa ga nasara a zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni a mafi yawan jihohi. Sun faɗa masa su kansu wani ɓangare ne na nasarar da ya samu a babban zaɓe."

Kara karanta wannan

Ahaf: Tasgaro Ga Ganduje Yayin da Tsohon Gwamnan Arewa Ke Son Zama Shugaban APC

Yayin da aka tuntuɓe shi, Adamu ya tabbatar da cewa ya karɓi bakuncin gwamnonin, inda ya ce sun kawo masa ziyara ne domim jinjina masa, Within Nigeria ta rahoto.

"Ba Zancen N8k" Jerin Kayan Agajin da Gwamnatin Tinubu Zata Raba Wa Yan Najeriya

A wani rahoton kuma kun ji cewa gwamnatin Tinubu na yunkurin tallafa wa yan Najeriya a bangare daban-daban don rage raɗaɗin cire tallafin mai.

Majalisar ƙoli ta tattalin arziki a Najeriya ta yanke shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin rage wa yan Najeriya raɗaɗin cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262