Tinubu: Sanatan Anambra Ya Musanta Tura Sunayen Ministoci Ga Majalisar Dattawa

Tinubu: Sanatan Anambra Ya Musanta Tura Sunayen Ministoci Ga Majalisar Dattawa

  • Sanata Victor Umeh na mazaɓar Anambra ta Tsakiya ya musanta zuwan sunayen ministocin shugaba Tinubu hannun majalisar dattawa
  • Umeh ya ce majalisar datttawa ba ta tattauna kan sunayen ministocin ba a lokacin da ta shiga zaman sirri domin basu ƙariso gare ta ba
  • A ɗazu rahotanni sun nuna cewa ministocin shugaba Bola Ahmed Tinubu sun isa majalisar dattawa domin tantancewa da amince wa

FCT Abuja - Sanata mai wakiltar Anambra ta tsakiya, Sanata Victor Umeh, ya bayyana cewa har yanzu sunayen Ministocin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ba su ƙarisa majalisar dattawa ba.

A rahoton da jaridar Independent ta haɗa, Umeh ya ce labaran da ke yawo a soshiyal midiya cewa Ministocin sun isa majalisar dattawa ba gaskiya bane.

Sanatan Anambra ta tsakiya, Victor Umeh.
Tinubu: Sanatan Anambra Ya Musanta Tura Sunayen Ministoci Ga Majalisar Dattawa Hoto: @Senvictorumeh
Asali: Twitter

Ya tabbatar da cewa har yanzun majalisar ba ta karɓi sunayen Ministocin ba saɓanin yadda ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Majalisar Dattawa Ta Yi Magana Kan Sunayen Ministocin Shugaba Bola Tinubu

Sanatoci ba su tattauna kan Ministocin Tinubu ba

Sanata Umeh ya ƙara da cewa ko kaɗan majalisar dattawa ba ta tattauna kan Ministoci ba lokacin da Sanatoci suka shiga zaman sirri a zauren majalisa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu rahotanni a ɗazu, sun yi ikirarin cewa shugaban ƙasa ya miƙa sunayen ministocin da ya naɗa zuwa Majalisar Dattawa.

Sai dai fadar shugaban ƙasa ko majalisar dattawa ba su ce komai da nufin tabbatar da sahihancin labarin ba, kuma raɗe-raɗin ya karaɗe soshiyal midiya.

Yaushe shugaba Tinubu zai naɗa Ministoci?

Ana tsammanin Shugaba Tinubu ya aika sunayen ministocin da ya naɗa Majalisar Tarayya kafin ko ranar 27 ga watan Yuli, 2023 lokacin da zai cika kwana 60 da hawa mulki.

Wannan ya faru ne bisa la'akari da dokar da ta tilasta wa shugaban ƙasa da gwamnoni naɗa mambobin majalisar zartarwansu cikin kwanaki 60 na farko da hawansu mulki.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi Mummunan Hatsari a Hanyar Koma Wa Abuja

A baya, an samu rahoton cewa Tinubu ya tura sunayen Ministocin zuwa hukumar tsaron farin kaya DSS da hukumar yaƙi da rashawa EFCC domin tsaftace su.

Zaben Kogi: Dan Takarar Sanatan SDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC Mai Mulki

A wani rahoton kuma Ɗan takarar sanata a inuwar SDP a babban zaben 2023, Abdulrahman Tanko Ozi, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar Kogi.

Mr Tanko Ozi ya kara da cewa ya umarci magoya bayansa su mara wa ɗan takarar APC, Ahmed Ododo baya a zaɓen gwamnan Kogi da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262