Wanda Ya San Ciki da Wajen APC, Ya Haska Kuskuren Tsohon Shugaban Jam’iyya 3
- Lanre Isa-Onilu yana ganin Abdullahi Adamu ya jawowa kan shi duk abin da ya faru a jam’iyyar APC
- Tsohon Sakataren yada labaran na APC ya jero kura-kuran da ya ce tsohon shugaban jam’iyyar ya yi
- Bayan Adamu ya gaza cigaba da sasanta ‘yan jam’iyya, ta kai yana ya yi fito na fito da shugaban kasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Lanre Isa-Onilu ya tofa albarkacin bakinsa a kan abubuwan da su ke faruwa a APC da har ya kai ga shugaban jam’iyya ya ajiye matsayinsa.
Lanre Isa-Onilu wanda ya taba zama Sakataren yada labarai a jam’iyyar APC, ya zanta da Vanguard kan rikicin cikin gidan da ya barko masu.
A ra’ayin tsohon kakakin na APC mai-mulki, babban kuskuren Sanata Abdullahi Adamu bayan ya karbi shugabanci shi ne watsi da shirin sulhu.
Ba a sasanta rikicin gida ba
Isa-Onilu yake cewa Adamu yana maye gurbin Mai Mala Buni a majalisar NWC, sai ya ajiye batun sasancin da ake ta kokarin yi tun kafin ya shiga ofis.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shi karon kan shi, Adamu ne ya jagoranci wannan kwamiti da aka kafa domin a dinke baraka.
Goyon bayan 'Ahmad Lawan'?
Bayan maganar yi wa ‘yan jam’iyya da ke rikici sulhu, ‘dan siyasar ya ce Adamu ya yi kuskure wajen goyon bayan wani ‘dan takara a zaben gwani.
"A matsayin shugaban APC, za ayi tsamannin ba zai nuna bambanci a jam’iyya ba. Ya kamata ya zama bai dauki bangare ba, amma bai yi ba.
A lokacin zaben tsaida gwani, sai aka samu shugaban jam’iyya da ya zama babban mai goyon bayan wasu ‘yan takara, hakan ya saba ka’ida.
Hakan bai dace da shi a matsayin shugaban na kasa ba. Ba za ka iya ba mutanenka kwarin gwiwa, a amince da kai idan ka nuna ra’ayi ba.
- Lanre Isa-Onilu
Fito na fito da Bola Ahmed Tinubu?
Domin maidawa Sanata Adamu martani ne, Isa-Onli yake tunanin Bola Tinubu ya fito da taken “Emi Llokan”, yana nufin cewa yanzu lokacinsa ne.
A wasu lokutan kuwa, rahoton ya ce jigon na APC ya zargi tsohon shugaban jam’iyyar da yi wa Tinubu rashin adalci ko nuna bai tare da shi.
Bayan an tsaida shugabannin majalisa, sai aka ji Adamu yana neman yin fito na fito, a maimakon sulhu ta bayan fage, Isa-Onile ya ce hakan raini ne.
Sabon shugaban jam'iyyar APC
Rahoto ya zo cewa Abdullahi Umar Ganduje zai rike jam’iyyar APC mai mulki, da alama an fasa ba tsohon Gwamnan Jihar Kano kujerar Minista.
Hankalin Bola Tinubu da manyan APC ya kwanata da Ganduje a maimakon wani tsohon Gwamna da ya fito daga yanki daya da Abdullahi Adamu.
Asali: Legit.ng