Shugaban Kasa Tinubu Ya Bai Wa Abdullahi Abbas Mukami a Gwamnatinsa

Shugaban Kasa Tinubu Ya Bai Wa Abdullahi Abbas Mukami a Gwamnatinsa

  • Shugaban kasa Tinubu ya aika sunayen wasu mutane domin tabbatar da su a hukumar bunkasa ci gaban arewa masu gabas (NEDC)
  • Tinubu ya aika sunayen gaban majalisar dattawa a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli don nada su a mukamai daban-daban
  • Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya samu shiga a matsayin mamba

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mambobi da shugaban majalisar hukumar bunkasa ci gaban arewa masu gabas (NEDC).

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa Tinubu ya nada shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a matsayin wakili a majalisar daraktocin hukumar ta NEDC.

Shugaban kasa Tinubu ya baiwa Abdullahi Abbas mukami
Shugaban Kasa Tinubu Ya Bai Wa Abdullahi Abbas Mukami a Gwamnatinsa Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Bukatar shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio kuma ya karanto ci a zaman majalisar a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya Yayin da Rikicin APC Ya Yi Kamari

A cikin wasikar da ya aika, shugaban kasar ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daidai da sashi na 5(b) na dokar hukumar bunkasa ci gaban arewa maso gabas na 2017.
"Na rubuto wasikar don majalisar dattawa ta tabbatar da nadin shugaba, mambobi da daraktocin hukumar bunkasa ci gaban arewa maso gabas."

Jerin sunayen wadanda Tinubu yake so majalisa ta tabbatar a hukumar NEDC

Sunayen wadanda za a tabbatar sun hada da Paul Tarfa, shugaba (Arewa maso gabas, Adamawa), Gambo Maikomo mamba (Arewa maso gabas, Taraba), Abdullahi Abbas mamba (Arewa maso yamma, Kano).

Sai Tsav Aondoana mamba (Arewa ta tsakiya, Benue), Mutiu Lawal- Areh mamba (kudu maso yamma, Lagos), Samuel Onuigbo mamba (Kudu maso gabas, Abia).

Sauran sune Frank Owhor, member (kudu maso kudu, Rivers), Mohammad Alkali (Manajan Darakta, Arewa maso gabas, Borno) da Musa Yashi, Daraktan Gudanarwa na sashen bada tallafi (Arewa maso gabas, Bauchi).

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito: An Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Ya Ke Son Nada Wa Minista Daga Jihar Ogun

Ahmed Yahaya Daraktan Gudanarwa na sashen ayyukan yau da kullum, (Arewa maso gabas, Gombe, Abubakar Iliya, Daraktan mulki da harkokin kudi.(Arewa maso gabas, Yobe)..

Tinubu ya ce wakilai biyu daga ma'aikatar kudi da tsare-tsaren kasa za su cika mambobin hukumar, kanmar yadda doka ta tanadar.

Ana rade-radin nada Ganduje a matsayin shugaban APC

A wani labari na daban, mun ji cewa alamu masu ƙarfi da suka fito da yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, sun nuna wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke son ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC.

An tattaro cewa alamun sun nuna Tinubu ya karkatar da hankalinsa kan tsohon gwamnan Kano, dakata Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng