“Yan Najeriya Za Su Taka Rawa Da Tsalle a Titi Idan Aka Soke Zaben Tinubu”, PDP
- Jam'iyyar PDP ta yi hasashen makomar shugaban kasa Bola Tinubu a kotun zabe
- Gabannin yanke hukuncin kotun, PDP ta bayyana cewa yan Najeriya za su yi rawan murna idan kotu ta soke nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 15 ga watan Fabrairu
- Pedro Obaseki, daraktan dabaru da bincike na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, shine ya yi wannan hasashen a wata sanarwa a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa ta bayyana abun da zai faru idan kotun zaben shugaban kasa ta soke nasarar zaben jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Abun da yan Najeriya za su yi idan kotu ta tsige Tinubu, PDP ta bayyana
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa yan Najeriya za su fita tituna don murna idan kotu ta soke nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa Pedro Obaseki, daraktan dabaru da bincike na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, shine ya yi wannan hasashen a Abuja a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nasarar Tinubu: PDP ta nuna karfin gwiwa a kan bangaren shari'a gabannin hukuncin karshe da kotun zabe za ta yanke
Obaseki, wanda ya yi jawabi ga manema labarai gabannin hukuncin kotun zabe, ya kuma nuna karfin gwiwar cewa PDP ta yi amanna da bangaren shari'a na yanke hukunci na gaskiya wanda bangarorin da abun ya zaba za su yarda da shi, jaridar The Guardian ta rahoto.
Ya kuma ce saboda nauyin hujjar da suke da shi, alkalan kotun zaben za su samu karfin gwiwar magance matsalolin da suka taso, inda ya ce martabar kasar na cikin hadari, a cewarsa alkalan ba za su yi wasa da haka ba.
Tinubu na shirin daura Ambode a kujerar sanatan Lagas
A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana duba yiwuwar dawowa da tsohon gwamnan jihar Lagas, Akinwunmi Ambode, a harkokin siyasa.
Majiyoyi da ke da masaniya kan ci gaban sun bayyana cewa shugaban kasar na duba yiwuwar ganin tsohon gwamnan ya zama sanatan Lagas ta gabas yayin da za a yi wa wanda ke rike da mukamin a yanzu, Tokubo Abiru, dannar kirji da mukamin minista.
Asali: Legit.ng