APC Na Duba Yuwuwar Maye Gurbin Adamu da Ganduje a Matsayin Shugaba
- Ga dukkan alamu shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya fi natsuwa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya maye gurbin shugaban APC
- Wasu alamu masu karfi da suka bayyana da yammacin Laraba sun nuna har an cire sunan Ganduje daga jerin ministoci
- Wannan na zuwa ne bayan Abdullahi Adamu ya yi murabus daga kujerar shugaban APC na ƙasa
FCT Abuja - Alamu masu ƙarfi da suka fito da yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, sun nuna wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke son ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC.
Rahoton jaridar Vanguard ya tattaro cewa alamun sun nuna Tinubu ya karkatar da hankalinsa kan tsohon gwamnan Kano, dakata Abdullahi Umar Ganduje.
Ga dukkan alamu shugaba Tinubu ya aminta Ganduje ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa.
Jaridar ta tattaro cewa sakamakon haka har an cire sunan Ganduje daga cikin jerin sunayem Ministocin da shugaban ƙasa Tinubu ke dab da miƙa wa majalisar tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaba da sakataren APC sun yi murabus
Idan baku manta ba shugaban APC ta ƙasa, Sanata Abbdullahi Adamu, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa ga ofishin shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Kwanaki kaɗan bayan haka, jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa Adamu tare da sakataren jam'iyya na kasa, Sanata Iyiola Omisore sun yi murabus daga kujerunsu.
Bisa haka kwamitin gudanarwa na APC (NWC) ya kira mambobinsa taron gaggawa ranar Litinin da ta gabata, inda aka ɗora Abubakar Kyari, a matsayin mukaddashin shugaban APC.
APC ta ɗage taron NEC sai baba ta gani
Bayan haka ne APC ta sanar cewa ta ɗage manyan tarukanta da ta tsara gudanarwa a ranakun 18 da 19 ga watan Yuli, 2023 har sai baba ta gani.
A cewar muƙaddashin shugaban APC, Abubakar Kyari, nan ba da jima wa ba zasu sanar da sabuwar ranar taron shugabanni da taron majalisar zartarwa (NEC).
Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na APC Zasu Gana da Gwamnoni a Abuja
A wani labarin na daban kuma shugabannin APC zasu gana da gwamnonin PGF a Abuja kan sabbin abubuwan da suka faru a kwanan nan.
Wannan taro na zuwa ne awanni 48 kacal bayan mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa, Abubakar Kyari, ya karbi ragamar jam'iyya a matsayin muƙaddashin shugaba.
Asali: Legit.ng