Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani Kan Tsadar Mai, Ta Ce Bai Kamata 'Yan Najeriya Su Sayi Lita Fiye Da N150 Ba

Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani Kan Tsadar Mai, Ta Ce Bai Kamata 'Yan Najeriya Su Sayi Lita Fiye Da N150 Ba

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta koka kan yadda gwamnatin APC ta gaza a mulkinta
  • Jam'iyyar ta ce duk da cire tallafin man fetur a kasar, bai kamata 'yan Najeriya su sayi litar mai fiye da N150 ba
  • Kakakin jam'iyyar, Debo Ologunagba shi ya bayyana haka inda ya ce wannan tashin farashin tsokana ce ga 'yan Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Jam’iyyar adawa ta PDP ta koka kan yadda farashin litar mai ta karu inda ta ce hakan tsokanar ‘yan Najeriya ake son yi.

Jam’iyyar ta ce bai kamata ‘yan Najeriya su sayi litar man fetur fiye da N150 ba duk da cewa an cire tallafin man a kasar.

Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani Kan Tsadar Mai, Ta Ce Bai Kamata A Saya Fiye Da N150 Ba
Jam'iyyar PDP Mai Adawa Ta Soki Salon Mulkin APC, Ta Koka Kan Yadda 'Yan Kasar Ke Shan Wahala. Hoto: TheCable.
Asali: Twitter

Kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba shi ya bayyana haka a jiya Talata 18 ga watan Yuli inda ya ce farashin ya yi muni, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Na Kwanaki 2 Kadai A Sati Bayan Cire Tallafi

Ya ce ‘yan Najeriya na rasa hanyoyin cin abincinsu saboda wannan gaggawar gaddamar da abubuwa na gwamnatin APC ba tare da shawara ba, Platinum Times ta tattaro

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jam'iyyar PDP ta kadu da yadda gwamnatin APC ke gudanar da abubuwa cikin gaggawa.
"Gwamnatin ta na gudanar da mulki yayin da tattalin arzikin kasar da harkokin kasuwanci ke faman durkushewa.
"Wannan hali da ake ciki ya nuna rashin iya mulki na jam'iyyar da kuma cin hanci da ya yi katutu, da kuma rashin kwarewa wurin tafiyar da tattalin arziki.

Ta bayyana yadda ta gudanar da mulki ga 'yan Najeriya cikin sauki

Ya kara da cewa:

"PDP ta yi fatali da hujjar cewa tsadar mai din na da alaka da yanayin kasuwa da kuma kwatanta farashin da sauran kasashe.
"A lokacin PDP, duk da cire tallafin a albarkatun mai, gwamnatin PDP ta yi kokarin gyara al'amura da ke da alaka da matatan mai.

Kara karanta wannan

Akpabio Ya Magantu Kan Batun Karin Albashin Ma’aikata, Ya Kuma Bayyana Dalilin Cire Tallafin Man Fetur

"Bai kamata duk tsadar litar mai ta wuce N150 ba."

Jigon PDP Ya Ce Najeriya Ta Shiga Halin Da Take Ciki Saboda Kwaikwayon Amurka

A wani labarin, jigon jam'iyyar PDP, Bode George ya bayyana dalilin da ya sa Najeriya ta shiga halin da ta ke ciki.

George ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban bako a wajen wata lakca da 'SWAAYA Limited' ta gudanar a Abuja.

Ya ce al'amuran kasar ba sa tafiya dai-dai saboda ta kwaso kundin tsarin kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.