Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na APC Zasu Gana da Gwamnoni a Abuja

Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na APC Zasu Gana da Gwamnoni a Abuja

  • Kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (NWC) ya shirya zama da gwamnonin jam'iyya mai mulki yau Laraba a Abuja
  • Wannan gana wa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan shugaban APC da Sakatare sun yi murabus daga muƙamansu
  • NWC ya shirya wannan taro ne domin tattauna batutuwa masu muhimmanci da kuma inda aka dosa a APC

FCT Abuja - Mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na jam'iyyar APC ta ƙasa zasu sa labule da gwamnonin jam'iyyar yau Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a birnin Abuja.

Rahoton The Nation ya ce NWC zata gana da gwamnonin ne a wani yunƙuri na neman goyon baya daga manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC bayan murabus ɗin Abdullahi Adamu.

NWC zai gana da gwamnonin APC yau a Abuja.
Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na APC Zasu Gana da Gwamnoni a Abuja Hoto: OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Wannan taro na zuwa ne awanni 48 kacal bayan mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa, Abubakar Kyari, ya karbi ragamar jam'iyya a matsayin muƙaddashin shugaba.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

Hakan ta faru ne bayan shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da sakatare na ƙasa, Iyiola Omisore sun yi murabus daga kan muƙamansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa NWC ta shirya zama da gwamnoni?

A wurin taron da NWC ya gudanar ranar Litinin, an cimma matsayar zama da masu ruwa da tsaki kan abubuwan da ke faruwa a cikin gida.

Haka zalika kwamitin na son jin ta bakinsu dangane da taron shugabanni da kuma taron majalisar zartarwan APC na ƙasa da ke tafe nan gaba kaɗan.

Vanguard ta ruwaito cewa sabbin shugabannin APC na kokarin yadda za a yi su samu zama da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, saboda komai ya far lokacin yana Kenya

Yaushe NWC zai samu zam da mambobin PGF?

Wani mamban kwamitin NWC, wanda ya tabbatar da shirya taron, ya ce:

"Ganawar da zamu yi yau da gwamnoni wani ɓangare ne na kokarin jawo dukkan masu ruwa da tsaki a APC don tattauna abinda ke faruwada kuma inda muka dosa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar APC Ya Ɗau Zafi, Ta Ɗage Muhimman Taruka 2 Bayan Murabus Ɗin Adamu

"Ina mai faɗa muku ceqa taron zai gudana yau (Laraba) daga nan zuwa anjima. Tun a taron mu na ranar Litinin muka cimma wannan matsayar."

Majaisa Ga Tinubu: Ka Yaye Takunkumin Daukar Ma'aikata a Najeriya

A wani rahoton na daban Majalisa ta bukaci shugaba Tinubu ya cire takunkumin ɗaukar ma'aikata aiki a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

A cewar majalisar, shekaru da dama da suka shuɗe tsohon shugaban ƙasa ya kakaba takunkumin sakamakon matsin tattalin arzikin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262