Hukumar INEC Ta Gaza Kare Nasarar Gwamnan PDP a Gaban Kotun Zabe
- Hukumar INEC ta gaza gabatar da shaidu domin kare kanta da tabbatar da nasarar gwamnan Enugu na PDP a zaben 2023
- A ci gaba da zaman Kotun zaɓe ranar Laraba, Lauyan INEC ya ce hukumar ta yi mazari kuma ta fasa gabatar da shaidu
- A halin yanzu Kotun ta ɗaga zaman da awa 2 domin PDP ta shirya fara gabatar da shaidu da misalin ƙarfe 11:00 na safe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Enugu state - Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gaza kare nasarar gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, na jam'iyyar PDP a gaban kotun zaɓe.
Rahoton The Nation ya nuna cewa INEC ta gaza kare tuhumar da ɗan takarar gwamna na Labour Party, Chijioke Edeoga, ya yi a Kotu cewa an tafka magudi a zaɓen gwamnan Enugu 2023.
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan ta ci gaba da zama domin bai wa hukumar INEC damar gabatar shaidunta da zasu gamsar da sahihancin zaɓen da ya ba Peter Mbah nasara.
Sai dai lokacin da aka dawo zaman sauraron ƙarar, INEC ta hannun tawagar lauyoyinta karkashin Humphrey Okoli ta faɗa wa Kotu cewa ta fasa kiran shaidu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Okoli ya ce:
"Wanda ake tuhuma ta farko watau INEC ce zata kare kanta a halin yanzu, amma bayan nazari kan Kes din hukumar ta yanke shawarar ba zata gabatar da ko shaida ɗaya ba."
Wane mataki jam'iyyar PDP ta ɗauƙa kan haka?
A bangarensa, lauyan PDP, Benjamin Nwosu, da kuma lauyan gwamna Mbah ba su yi musu da matakin INEC ba. Ana tsammanin PDP zata fara kare kanta nan ba da jima wa ba.
Jam'iyyar PDP ta nuna cewa ta shirya tsaf zata gabatar da shaidu domin tabbatar da sahihancin sakamakon zaben gwamna, wanda ta lashe a 2023.
PDP ta nemi ƙarin lokaci
Sai dai a halin yanzu jam'iyyar ta gaya wa Kotun sauraron ƙarar zaben cewa tana buƙatar karin lokaci domin samun damar gabatar da kwararan shaidun da ta tanada.
A rahoton Daily Post, Lauyan PDP ya ce:
"Mun shirya fara kare kanmu yau. A yanzu muna rokon Kotu ta ƙara mana awanni biyu gabanin fara gabatar da shaidun mu."
Bayan wannan roko kuma lauyan Edeoga bai yi musu ba, Kotu ta ɗaga zaman da awanni 2, PDP zata fara gabatar da shaidunta da ƙarfe 11:00 na safiyar yau Laraba.
Shema da Tawagarsa Sun Ziyarci Gwamna Dikko Radda a Katsina
A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda ya karɓi bakuncin tsohon gwamna, Ibrahim Shema a gidan gwamnatinsa.
Gwamna Radda ya gode wa Shema bisa gudummuwar da ya bai wa APC har ta samu nasarar lashe zaɓe ranar 18 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng