Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya Makon Nan

Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya Makon Nan

  • A wannan makon shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aika sunayen ministoci ga majalisar tarayya domin tantance wa
  • Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta ce tsakanin ranakun Laraba da Alhamis ake tsammanin sunayen ministocin zasu isa majalisa
  • Kwanaki 10 suka rage wa shugaba Tinubu ya naɗa ministoci bisa la'akari da dokar da ta bai wa shugaban ƙasa kwana 60 bayan hawa mulki

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tura sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa a makon nan matuƙar ba a samu sauyi da ka iya kawo cikas ba.

Wasu majiyoyi masu ƙarfi daga fadar shugaban ƙasa sun nuna cewa tun da jima wa Tinubu ya gama tsara ministocinsa amma an samu wasu 'yan sauye-sauye daga baya.

Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Zai Mika Sunayen Ministoci Ga Majalisar Tarayya Makon Nan Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa wata majiya a fadar shugaban ƙasa, wacce ta nemi a sakaya bayanantaa, ta shaida cewa:

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Abdullahi Adamu Ya Rasa Mukamin Shugabancin APC

"Tun tuni da daɗe wa aka gama rubuta sunayen Ministoci amma daga baya shugaban ƙasa ya yi wasu sauye-sauye a wasu jihohi."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna tsammanin za a tura sunayen ministocin ga majalisar tarayya tsakanin ranar Laraba da Alhamis matuƙar ba a samu wani ci gaba da ka iya kawo ƙarin jinkiri ba."
"Ana tsammanin shugaban ƙasa ya naɗa mukarrabansa kafin ranar 26 ga watan Yuli, 2023 kuma ina da tabbacin za a tura sunayen ga majalisar dattawa a makon nan."

Idan baku manta ba a kwanakin bayan an yaɗa wasu sunaye da ake tsammanin sune Ministoci yayin da shugaban ƙasa ya bar yan Najeriya suna kintace kan waɗanda zai naɗa.

A halin yanzu ana dakon jiran a gani ko Tinubu zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa kamar yadda ake hasashe a wasu sassan ƙasar nan, TVC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa Daga Shugabancin APC, Ya Bayyana Mataki Na Gaba

Abinda kundin mulki ya tanada

Dokar ƙasa ta tanadi cewa wajibi shugaban ƙasa ya miƙa sunayen waɗanda zai naɗa ga majalisar tarayya cikin kwanaki 60 da hawa kan madafun iko.

Bisa la'akari da haka, Gwamnatin Tinubu ta karɓi rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, 2023, lokacin da Muhammadu Buhari ya miƙa ragamar mulki ga Tinubu.

Sakamakon abinda kwansutushin ya tanada na kwanaki 60, a yanzu kwana 10 ya rage wa shugaban ƙasa ya naɗa majalisar zartarwansa.

Farashin Litar Man Fetur Ya Ƙara Tashi a Najeriya, Ya Haura N600 a Gidan Man NNPC

A wani rahoton na daban kuma Farashin litar man fetur ta ƙara tashi daga N539 zuwa sama da N600 a tsakiyar birnin tarayya Abuja da safiyar Talata.

Har yanzun mahukunta ba su bayyana dalilin wannan ƙari ba amma ana ganin wataƙila yana da alaka da hasashen yan kasuwa cewa lita ka iya kai wa N700.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Har Yanzu Bai Tare a Gidansa na Villa Ba, An Bayyana Muhimmin Dalilin Da Ya Janyo Hakan

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262