Daga Ajiye Mukaminsa a APC, An Jibge Jami’an Tsaro a Gidan Abdullahi Adamu
Akwai yiwuwar cewa akwai sauran danyen aiki a gaban Abdullahi Adamu duk da ya yi murabus
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
An fara ganin jami’an tsaro a gidan shi yayin da masu yawan kai ziyara su ka fara dauke kafafunsu
Watakila Hukumar EFCC tayi binciken kan zargin da ake yi na facaka da N30bn a jam’iyyar APC
Abuja - Kwana guda da ya gabatar da takardar murabus, sai ga shi an aiko da jami’an tsaro zuwa gidan tsohon shugaban APC, Abdullahi Adamu.
Binciken Daily Trust ya nuna an ga jami’ai sun yi zuru-zuru a ranar Litinin a gidan Abdullahi Adamu wanda ya shugabanci jam’iyyar APC mai-ci.
Da kimanin karfe 3:00 na rana aka hangi jami’an tsaro masu fararen kaya su na sintiri a gidan tsohon Gwamnan da ke kan titin Ali Akilu a Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gidan Adamu bai da nisa da Aso Rock
Gidan sa yana kan hanyar zuwa fadar shugaban kasa Aso Rock da ke babban birnin na tarayya.
Daga nesa ana hangen mutanen da ke gidan su na harkokin gabansu kamar babu abin da ya faru sai dai an samu raguwar hayaniya da masu ziyara.
EFCC sun fara kawo ziyara
Jaridar ta ce ma’aikatan hukumar EFCC masu yaki da rashin gaskiya sun ziyarci gidan tsohon Gwamnan na Nasarawa tun kafin a ga jami’an tsaro.
Da aka nemi jin ta bakin EFCC, ba ayi dace ba domin kuwa kakakinsu na kasa, Wilson Uwujaren bai amsa kiraye-kirayen wayar da aka yi masa ba.
A daren yau, wata majiya ta shaida cewa yanzu haka akwai korafi da aka gabatarwa EFCC a game da Adamu, kuma ana sa ran a fara bincike a kai nan-take.
Ana zargin APC a karkashin jagorancin Sanata Adamu da sakatarensa watau Omisore tayi facaka da Naira Biliyan 30 da aka tara daga kudin fam.
Hakan na zuwa ne bayan abin da ya faru a Sakatariyar jam’iyyar da ke garin Abuja, inda aka sanar da tafiyar Abdullahi Adamu da kuma Iyiola Omisore.
Sanata Iyiola Omisore ya isa babban ofishin jam’iyyar a mota, amma bai dade ba ya yi tafiyarsa. Wasu majiyoyi sun ce an hana shi halartar taron NWC.
DSS da Sarkin Hausawan Legas
Hankalin majalisar Sarakunan Arewan ya kai ga cigaba da tsare Sarkin Hausawan Legas da ake yi, rahoto ya zo cewa Jarman Legas ya fitar da jawabi.
DSS ta cafke Aminu Idris Yaro ba tare da an yi wa jama’a bayani ba, jama'a su ana zargin an kama shi ne saboda alakarsa da Mista Godwin Emefiele.
Asali: Legit.ng