“Ya Dauki Hanyar Adams”: Shehu Sani Ya Yi Martani a Kan Murabus Din Adamu
- Sanata Shehu Sani ya yi martani a kan murabus din Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa
- Tsohon dan majalisar ya lissafa muhimman abubuwa biyu da suka yi sanadiyar ficewar tsohon gwamnan na jihar Nasarawa
- Sani ya ambaci ambaci lokacin da Adamu ya ayyana Lawan a matsayin dan takarar maslaha na APC da kuma rashin masaniya a kan jerin sunayen shugabannin majalisa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya ta 8, ya lissafa wasu manyan laifuka biyu da suka yi sanadiyar murabus din Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.
Sani ya ce abu na farko shine lokacin da Adamu ya sanar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar maslaha na APC amma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar shi a tsaka mai wuya kafin babban taron jam'iyyar na kasa a 2022.
Ya ce abu na biyu shine Adamu bai da masaniya a kan jerin sunayen shugabannin majalisar dokoki na 10 da aka amince da su.
Ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter mai suna @ShehuSani a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, yana mai cewa wadannan abubuwa guda biyu sun nuna cewa Adamu na cikin yanayi mai wuyar sha'ani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Daga lokacin da ya sanar da Lawan a matsayin dan takarar maslaha na jam'iyyar mai mulki sannan Buhari ya bar shi a tsaka mai wuya, zuwa lokacin da aka bar shi a cikin duhu kan jerin sunayen manyan jami'an majalisar dokoki na kasa da aka aminta da su, na san cewa Adamu zai bi hanyar Adams."
Shugaban jam'iyya na kasa: An shawarci APC da ta nada Abdullahi Ganduje a kan kujerar Abdullahi Adamu
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu sun fara yin kira ga jam’iyyar APC mai mulki ta nada Abdullahi Umar Ganduje ya zama sabon shugaba na kasa.
Legit.ng Hausa ta bibiyi shafukan sada zumunta, ta gano akwai masu wannan ra’ayi. Wadanda su ke ganin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dace ya maye gurbin Abdullahi Adamu, sun yaba da yadda yake kaunar APC.
Asali: Legit.ng