Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Abdullahi Adamu Ya Rasa Mukaminsa
- Ta tabbata matsala Abdullahi Adamu ya hango tana tunkararsa shiyasa ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC
- Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, shi ne ya shawarci shugaban na APC da ya yi murabus bayan ta tabbata ana shirin tsige shi
- Ana dai zargin Abdullahi Adamu da salwantar da maƙudan kuɗi har N32bn da jam'iyyar ta samu wajen siyar da fom ɗin takara lokacin zaɓe
FCT, Abuja - An shawarci shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da ya yi murabus daga muƙaminsa bayan ya daɗe yana tsama da Shugaba Bola Tinubu, rahoton The Cable ya tabbatar.
Shugaban gwamnonin jam'iyyar APC (PGF), kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, shi ne ya shawarci Abdullahi Adamu da ya yi murabus daga muƙaminsa.
Iyiola Omisore, sakataren jam'iyyar APC na ƙasa sai ya shiga wasan ɓuya bayan ya samu labarin abinda ke faruwa.
Da Dumi-Dumi: Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa Daga Shugabancin APC, Ya Bayyana Mataki Na Gaba
Majiyoyi daga cikin jam'iyyar sun gayawa TheCable cewa mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) za su kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa da Adamu da Omisore a ranar Litinin, inda za a tsige su a ranar Laraba wajen taron majalisar zartaswa ta jam'iyyar wanda Shugaba Tinubu zai jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai dai ƴar tsama a tsakanin Shugaba Tinubu da Abdullahi Adamu tun bayan da tsohon gwamnan na jihar Nasarawa ya zama shugaban jam'iyyar APC a watan Maris na shekarar 2022.
Dalilin da ya sanya Adamu ya rasa muƙaminsa
Amma batun ƙarshe da ya janyo matsala ga Adamu shi ne, yadda ya kasa bayar da sahihan bayanai kan N32bn da jam'iyyar ta tattara ta hanyar siyar da fom ɗin takara na babban zaɓen 2023.
"N7bn kawai ta rage a asusun yanzu haka da mu ke magana." A cewar wani mamban NWC.
Jaridar ta bayyana cewa lokacin da aka kai batun N32bn zuwa ga Shugaba Tinubu, ya amince da a tsige Adamu ta hanyar da doka ta tanada.
Uzodinma ya tuntuɓi Adamu a ranar Lahadi inda ya buƙace shi da ya yi abinda ya dace amma bai samu damar tuntuɓar Omisore ba.
Abdullahi Adamu Ya Yi Magana Kan Murabus Dinsa
Rahoto ya zo cewa Abdullahi Adamu ya yi magana kan batun murabus ɗin da ya yi daga shugabancin jam'iyyar APC.
Shugaban na jam'iyyar APC ya bayyana cewa sai bayan Shugaba Tinubu ya dawo gida Najeriya zai yi magana kan murabus ɗin nasa.
Asali: Legit.ng