Tinubu Na Dab Da Sanya Hannu Kan Kudirin Karawa Ma'aikata Albashi Zuwa 200k

Tinubu Na Dab Da Sanya Hannu Kan Kudirin Karawa Ma'aikata Albashi Zuwa 200k

  • Shugaba Bola Tinubu na shirin sanya hannu kan kudurin yi wa ma'aikatan Najeriya karin albashi mai tsoka
  • Ana sa ran shugaban zai sanya hannu kan kudurin da kungiyoyin kwadago suka kai masa na kara albashin zuwa N200,000
  • Tinubu ya taba ikirarin cewa ma'ikatan gwamnati za su sami albashin da zai ishesu gudanar da rayuwa cikin walwala

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya za ta amince da ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N200k duk wata kamar yadda kungiyoyin suka bukata.

Sai dai kuma gwamnonin Najeriya ba su goyi bayan matakin ɗari bisa ɗari ba domin kuwa sun ba Gwamnatin Tarayya shawarar cewa a dai bi abin a sannu.

Shugaba Tinubu na shirin karawa ma'aikata albashi zuwa 200k
Tinubu shirin sanyawa kudurin kara albashin ma'akata zuwa 200k hannu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya gamsu da bayanan da aka masa kan karin albashin ma'aikata

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Kamar yadda jaridar Leadership ta yi rahoto, an tattauna batun ne a taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da ya gudana a watan jiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wajen taron, hukumar kula da albashin ma’aikata ta gabatar da wani bayani kan yadda gwamnatin tarayya za ta iya biyan naira 200,000 matsayin mafi karancin albashi a wata.

Wata majiya ta bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya gamsu da bayanan da kungiyar ta yi masa, musamman in aka yi waiwaye ga alkawuran da ya yi lokacin yakin nemam zabe.

Gwamnoni sun cewa Gwamnatin Tarayya ta yi taka tsan-tsan kan karin albashi

Premium Times ta yi wani rahoto a baya, inda Shugaba Tinubu ya taba bayyana cewa, ma'aikata za su samu wadataccen albashin da zai ishesu gudanar da rayuwarsu cikin walwala tare da iyalansu.

Kara karanta wannan

A banza: Sanata Sani ya kushe tafarkin Tinubu da Buhari kan toshe iyakokin kasa

Gwamnoni a karkashin wani kwamiti da gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ke jagoranta sun nuna cewa yana da kyau Gwamnatin Tarayya ta faragano ta inda za ta samu kudaden da za su ba ta damar aiwatar da karin.

Sai dai a mahangar gwamnatin ta Tinubu, Gwamnatin Tarayya da ta jihohi za su samu karuwar wadatar kudaden da za su yi amfani da su sakamakon sabuwar dokar da aka sanya kan hada-hadar kudaden kasar waje.

Haka nan kuma, gwamnatin ta Tinubu na hasashen cewa kudaden tallafin man fetur da ta cire zai taimaka wajen samar ma ta da karin isassun kudaden da za ta yi amfani da su wajen kara albashin ma'akata daga naira 30,000 zuwa sabon da za a yanke.

Ganduje ya yi wa Abba Gida Gida martani kan caccakar Tinubu da ya yi

Legit.ng a baya ta ruwaito muku cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci gwamna mai ci, Abba Gida Gida da ya bi sha'anin mulki a hankali.

Kara karanta wannan

Biliyan 500 Na Kayan Rage Radadi: Abba Gida-Gida Ya Ce Bai Soki Tinubu Ba

Shawarar na zuwa ne bayan caccakar da Abban ya yiwa Tinubu kan batun raba kudaden tallafi ga jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng